Shahararriyar marubuciya a masana’antar Kannywood kuma shugabar Gidauniyar Creatibe Helping Needy Foundation mai taimakawa masu karamin karfi da marasa lafiya,kuma babbar mai taimakawa gwamnan jihar Kano Eng Abba Kabir Yusuf akan masu bukata ta musamman Fauziyya D Suleiman.
Ta bayyana cewar masu yiwa masana’antar Kannywood kudin goro suna kiransu da yan iska su daina,domin kuwa masana’antar tanada mutane da yawa wadanda basu da rajistar zama yan kungiya,kuma suna neman suna ta hanyar yin shigar banza inda suke janyowa masana’antar zagi daga wajen mutane.
- Ana Amfani Da Na’urar Hakar Mai Ta Zamani Da Kamfanin Sin Ya Kera A Uganda
- Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Kashe Fiye Da Naira Biliyan 2 Domin Ciyarwa A Watan Ramadan
Fauziyya a wata hira da tayi da jaruma Hadiza Aliyu Gabon a cikin shirinta na Gabon’s Room Talk Show ta tabbatar da cewar a kowace irin masana’anta da ta tara dimbin mutane kamar Kannywood dole ne a samu mutane na kwarai da na banza ba a masana’antar kawai ba.
Daga karshe Fauziyya ta kara da cewar Kannywood ba wuri ne na gyaran tarbiyya ba kamar yadda mutane suke tunane,wuri ne wanda ake nishadantarwa da kuma ilmantar da mutane.