Biyo bayan cece-kuce kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke kan zaben gwamnan jihar Kano, kotun ta bukaci lauyoyin da su mayar da kwafin hukuncin da ta yanke domin ta yi gyara.
Babban Lauyan Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Haruna Isa-Dederi, a wani taron manema labarai ya ce, kwafin takardun hukuncin Kotun daukaka kara kan zaben Gwamnan Jihar ya tabbatar da nasarar Abba Kabir Yusuf a matsayin zababben Gwamnan Jihar Kano.
- Sanata Kaka Lawan Ya Gabatar Da Kudirin Tattara Dokokin Nijeriya Na Tsawon Shekara 19
- Kotun Daukaka Kara Ta Ce Tuntuben Alkalami Aka Samu Wajen Rubuta Kundin Hukuncin Shari’ar Zaben Kano
Ya kuma bayyana hukuncin da kotun ta yanke a matsayin “babban abin kunya” ga kotun.
A makon da ya gabata ne dai kotu ta kwace kujerar gwamnan Kano, Abba Yusuf, bisa hujjar cewa bai cancanci tsayawa takara ba.
Kotun ta bayyana cewa Yusuf, wanda ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar NNPP, ba dan jam’iyyar ba ne a lokacin zaben.
Kotun ta bayyana Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga watan Maris.