Za a iya cewa ba sabon abu bane a duk lokacin da aka samu labarin cewa daya daga cikin kungiyoyin da suke buga gasar firimiyar Nijeriya suna cikin matsalar kudi wadda har za ta iya sa wa kungiya ta kasa zuwa wasan da za ta fafata a waje saboda rashin kudin mota, abinci da kudin otel da na zirga-zirga.
Irin wannan matsalar ta zama Ruwan dare a gasar firimiya ta kasar nan kuma gwamnatoci da hukumomin da abin ya shafa har yanzu ba su fara daukar hanyoyin kawo karshen wannan matsala ba da ya kamata a ce tun farko an karkare ta duk da cewa idan aka ga dama za a iya kawo karshen matsalar.
A ranar Litinin daya ga wanann watan ne dai rahotanni daga Jihar Kano suka bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta gaza zuwa Jihar Abia, domin buga wasan gasar Firimiyar Nijeriya tsakaninta da takwararta ta Enyimba International ta garin Aba, da ke Jihar Abia saboda rashin kudi.
Wannan labarin ya tayar da hankalin magoya bayan kungiyar da ma duk wani mai sha’a war kwallon kafa a kasar nan saboda labari ne na karya zuciya da sake fito da rashin tabbas wajen ci gaban wasan kwallon kafa a Nijeriya.
Wasu rahotanni ne suka bayyana cewa, kungiyar wadda ake kira “SAI MASU GIDA” ba ta da kudin da za ta yi jigilar ‘yan wasanta da masu koyarwa zuwa jihar ta Abia kuma har ila yau wata majiya ta tabbatarwa da LEADERSHIP HAUSA cewa, rashin isassun kudi ne ya hana kungiyar tafiya buga wasan kuma daman a lokuta da dama kungiyar tana karbar aron kudi domin tafiya buga wasa a waje amma a wannan karon ta gaza samun bashin kudin.
Amma daga baya kuma aka fitar da sanarwar cewa gwamnatin Jihar Kano ta samu labari kuma ta bayar da umarnin ‘yan wasan su tafi Jihar Abia a jirgin sama, wanda kuma haka aka yi, tuni ‘yan wasan suka je a jirgi kuma ba a dage wasan ba, an yi a lokacin da aka tsara za a yi saboda daman rashin tafiya da wuri ne ya sa aka bukaci dage wasan.
Ba sabon labari ba ne
Sai dai matsalar rashin kudi a wajen kungiyoyin kwallon kafa a Nigeria ba sabon abu bane, inda ko a wannan kakar ma sai da aka dage wasan Kano Pillars da Abia Warriors saboda matsalar kudi da Abia ta shiga, sannan an taba dage wasan Gombe United da Remo Stars shima saboda rashin kudi a hannun kungiyar ta Gombe United.
Tun da farko ma dai sai da Kano Pillars ta rubuta wa hukumar da ke kula da gasar ta firimiyar Nijeriya cewa ba za ta iya zuwa wasan a kan lokaci ba kuma tana bukatar a dage wasan zuwa ranar Alhamis, maimakon ranar Laraba uku ga wannan watan da tun farko aka tsara amma daga karshe Pillars ta tafi garin Aba a jirgin sama kamar yadda wata majiya ta tabbatar wa da LEADERSHIP HAUSA
Sai dai ana ganin hakan ba mafita bace domin babu tabbas idan gwamnati za ta iya ci gaba da jigilar ‘yan wasa a jirgi a duk lokacin da za su buga wasa a wata jihar, kuma hasali ma akwai jihohin da ba su da filin jirgi da jirage suke sauka, dole sai dai a sauka a makobciyar jihar da jirage suke sauka da tashi daga baya su karasa a mota.
Shin wannan abin kunya?
Tabbas masu bibiyar harkar kwallon kafa a Nijeriya sun bayyana rashin jin dadinsu kuma sun tabbatar da cewa an tafka abin kunya domin kungiya kamar Kano Pillars tun farko ma bai kamata ta dinga dogaro da gwamnati ba wajen samun kudaden gudanarwa na yau da kullum idan har ana son ci gaban kungiyar yadda ya kamata.
Masu sukar suna ganin ya kamata shugabannin gudanarwar kungiyar su sani cewa, ba karamin abin kunya bane kana jagorantar kungiya kamar Kano Pillars amma ka dinga jira sai gwamnati ta baka kudin gudanarwa, wannan ya nuna gazawar shugabannin wajen kasa zamanantar da kungiyar da kuma fito da hanyoyin samun kudin shiga da za su taimaka wa kungiyar, watakila ma kungiyar ta dinga samar wa da gwamnati kudin shiga kamar yadda manya-manyan kungiyoyin duniya suke.
Sai dai daman shekara da shekaru masana tattalin arziki da masu bibiyar kwallon kafa a duniya baki daya suna da yakinin cewa kuskure ne a ce kungiya kamar Kano Pillars tana jira sai gwamnati ta ba ta kudi, idan aka yi duba da irin yawan ‘yan Kallon da suke shiga da kuma yawan magoya bayan kungiyar ba iya kawai a cikin Jihar Kano ba har ma da ragowar jihohi.
Tuni aka ba da shawarar cewa ya kamata shugabannin kungiyar su tashi tsaye su nemi masana domin a nemo hanyoyi da za a dinga samar da kudin shiga wanda hakan zai sa kungiyar ta rage dogaro da gwamnati, watakila ma ta fara biyan kanta albashi.
Wani bincike ma ya nuna cewa da yawa daga cikin ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ba ‘yan wasan kungiyar bane, domin yawancinsu na ejoji ne dake amfani da kungiyar wajen tallata ‘yan wasan wanda kuma a karshe ma idan dan wasa ya samu damar tafiya nahiyar Turai kungiyar ba ta samun kudi saboda tun farko dan wasan ba nata bane.
Rashin iya amfani da kafafen yada labarai na zamani.
Daya daga cikin matsalolin da kungiyar Kano Pillars take fuskanta shi ne rashin iya amfani da kafafen yada labarai musamman na zamani yadda ya kamata wajen tallata kungiyar da saka wasannin kungiyar a shafukan sada zumunta da saka yadda kungiyar take daukar horo da kuma tafiya tare da magoya baya ana jin ra’ayinsu sannan suma ana sauraron kokensu.
Kano Pillars za ta iya amfani da kafafen yada labarai musamman na zamani da suka hada da Youtube da tiktok wajen samun kudin shiga da kuma tallata kungiyar a santa a duniya baki daya.
Shin Kano Pillars za ta iya zama mai cin gashin kanta?
Wannan abu ne mai matukar wahala ba ma a kan kawai kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ba, gaba daya kungiyoyin da suke buga gasar Firimiyar Nijeriya saboda yawanci gwamnatocin jihohi ne suke rike su wanda kuma dole ne siyasa ta shiga.
Tabbas abu ne mai wahala gwamnati ta cire hannunta a harkar gudanar da kungiyoyi a kasar nan saboda yawanci gwamnatocin na amfani da kungiyoyin ne domin cimma bukatunsu na siyasa.
A Nijeriya kungiyoyin da ba mallakin gwamnati ba ba sa iya yin wani abin a zo a gani saboda rashin rashin kudi domin yawanci ‘yan kasuwa a Nijeriya ba su gama yarda cewa kwallon kafa babbar hanya bace ta kasuwanci kuma akwai zarge-zarge na cin hanci da rashawa da ya dabaibaye gasar wanda hakan na kara lalata abubuwa ta yadda zai yi wahala a samu wani ci gaba na a zo a gani domin dan kasuwa ba zai zuba kudinsa a inda babu tabbas ba.
Akwai kungiyoyin da ba na gwamnatocin jihohi ba musamman a kakar wasa ta shekara ta 2004 zuwa 2005 amma kawo yanzu da yawa daga cikinsu sun gaza saboda rashin kudi da kuma rashin tabbas a kan jagoranci da alkalancin wasanni.
Kungiyoyi na baya-bayan nan su ne kungiyoyin Ifaenyi Ubah da MFM kuma tuni sun gaza, sannan a wannan kakar ta bana ma akwai kungiyar Doma Utd ta Jihar Gombe, wadda ta fara da kyau a zangon farko amma tun da aka shiga zango na biyu abubuwa suka lalace mata saboda magana ce ta kudi.
Gwamnati tana iya yin kasafin kudi ta saka da kungiyar da take jihar kuma dole za a fitar da wannan kudin domin tafiyar da wannan kungiya amma shi dan kasuwa a kasuncinsa na yau da gobe yake samun kudin tafiyar da kungiya saboda haka idan ya ga baya samun riba dole zai ajiye ya nemi abin da zai kawo masa riba, ba kamar gwamnati ba wadda ita ba saboda riba take yi ba.
Yadda ake gudanar da gasar firimiyar Nigeria har yanzu ya kasa ba wa masu zuba jari dama domin su shigo su zuba kudi a kungiyoyi domin gasar ta gyaru hakan ya sa babu dan kasuwar da zai zuba kudinsa duk da kiraye-kirayen da ake yi.
Akwai bukatar a samu jagorancin hukumar dake kula da gasar ya kasance mai gaskiya, sannan akwai bukatar alkalan wasa su ma su kasance masu gaskiya sannan akwai bukatar samar da tsaro da hanyoyi da sauran abubuwan da za su sa a saka masu zuba jari su zo su sayi kungiyoyin kwallon kafa a kasar nan su zuba kudinsu domin a samu riba.
A kowace shekara, kowace kakar wasa abubuwan sake lalacewa suke domin kakar wasa ta karshe da aka buga wasa mai kyau kuma tsarkakakke ita ce kakar wasa ta 2007 zuwa 2008, gasar da Kano Pillars ta lashe, amma tun bayan wannan babu wata kungiya da ta cancanci lashe gasar kuma ta samu damar lashewa saboda tsabar zargin cin hanci da rashawa da kuma dogaro da gwamnatoci wajen samar da kudaden gudanar da kungiya.
Sannan su ma kungiyoyin suna bayar da gudunmawa wajen lalacewar gasar domin akwai zarge-zargen cewa suna tsorata alkalan wasa da rashin tsaro sannan kuma akwai zargin karbar na goro daga alkalan wasan da sauransu, kuma duk wannan yana daya daga cikin dalilan da suke sawa gasar ba ta samun ci gaba.
Idan har gwamnatocin jihohi suka zare hannayensu daga kungiyoyi tabbas gasar firimiyar kasar nan za ta sake lalacewa ne saboda rashin tabbas daga wajen masu zuba jari, ba wanda zai sayi kungiya sannan a ce sai kuma ya zo yana biyan cin hanci idan yana son ya samu nasara a wasa.