Gwamnatin jihar Kano ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta miko mata kasonta na rarar kudade daga tsarin iskar gas na Nijeriya (NLNG) na tsawon shekaru 25 da suka gabata.
A wata wasika da aka aika wa kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Hon. Ismail Falgore, Gwamna Abba Yusuf ya nemi majalisar ta shiga tsakani domin saukaka amso rarar kudaden wanda hakkin jihar Kano ne tun daga watan Janairun 1999 zuwa yau.
- Gwamna Sani Ya Mayar Wa Iyalan Abacha Filayen Da El-Rufai Ya Kwace Musu
- Tinubu Zai Ciyo Bashi Don Cike Gibin Naira Tiriliyan 13 A Kasafin Kudin 2025
A cikin wasikar da aka karanta a zauren majalisar a zaman majalisar na ranar Talata, gwamnan ya ce, in majalisar ta amince da kudurin, zai saukaka nemo maslaha don bin hanyoyin da suka da ce domin amso kudaden da aka tara na tsawon shekaru.
Ya yi nuni da cewa, idan aka amso kudaden, za su taimaka wajen kara karfin tattalin arzikin jihar tare da bai wa gwamnati damar magance muhimman abubuwan da ta sa a gaba domin amfanin al’umma.
Da yake mayar da martani kan wasikar, shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Husseini, ya jaddada cewa kudurin majalisar shi ne mabudin samun kudaden, yana mai bayyana cewa, hakan zai bai wa kungiyar gwamnoni damar daukar shawarwarin da suka dace domin amso kudaden. zuwa jihohi.
Ya kara da cewa, Makudan biliyoyin kudaden da ake shirin amsowa, za su yi tasiri a farfado da tattalin arzikin jihar domin amfanar al’umma idan aka amince da kudurin,