Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da bayar da tallafin Naira 500,000 ga kowane mahajjaci daga jihar.
Tallafin ya biyo bayan umarnin da Hukumar Alhazai ta kasa NAHCON ta bayar, inda ta bukaci maniyyatan da su biya karin Naira miliyan 1.9 na kudin Hajjin shekarar 2024.
- Dole Ne Mu Ajiye Bambancin Addini, Ƙabilanci Da Siyasa A Baya – Ministan Yaɗa Labarai
- Gwamnatin Nijeriya Ta Bayar Da Tirela 100 Na Shinkafa, Dawa Da Masara A Raba A Kano
Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Dan Baffa ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai ranar Laraba a Kano.
A cewarsa, gwamnatin jihar za ta biya jimillar kudi naira biliyan 1.4 ga maniyyata 2,096 da suka yi niyyar aikin hajjin bana.
Ya ce, gwamnatin jihar Kano ta dauki wannan matakin ne duba da karin kudin aikin Hajji da hukumar alhazai ta kasa ta yi a baya-bayan nan wanda a cewarta, karin an yi shi ne biyo bayan faduwar darajar Naira kan canjin Dalar Amurka.