Gwamnatin jihar Kano ta bayyana aniyarta na hadin gwiwa da kamfanin Afrinvest (West Africa) Limited domin inganta harkokin kasuwanci da ci gaban jihar.
Gwamna Abba Yusuf ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a bikin bude ofishin Afrinvest na Kano a ranar Alhamis.
- An Sulhunta Gwamnan Kano Da Sheikh Aminu Daurawa
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Makiyayi Da Shanu 35 A Wani Sabon Harin A Filato
Gwamnan wanda ya samu wakilcin Babban Sakatare a Ma’aikatar Kudi, Kabiru Sa’id Magami, ya bayyana cewa, babu wani lokaci da ya fi dacewa da Afrinvest ta kafa ofishi a jihar fiye da yanzu.
Gwamnan ya taya kungiyar Afrinvest murna kan nasarorin da ta samu a cikin shekaru 30 da suka gabata da kuma zaben Kano a matsayin daya daga cikin wuraren da ta kafa zango.
Gwamna Yusuf ya kuma yi alkawarin cewa, gwamnatin jihar za ta baiwa kamfanin duk wani tallafi da ya dace.