Mai riƙon ƙwarya na shugaba ƙaramar hukumar Shira da ke jihar Bauchi, Alhaji Wali Adamu, ya rasu.
Adamu ya rasu ne a ranar Lahadi a asibitin gwamnatin tarayya da ke Azare (FMC) a ƙaramar hukumar Katagum bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.
- 2027: PDP Ta Mutu, APC Na Shirin Sake Yin Nasara – Martanin Ganduje Ga Lamido
- Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Akasarin Jama’a Da Cudanyar Cinikayya Tare Da Sin Fiye Da Amurka
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa an naɗa Wali shugaban riƙon kwayar na Shira ne bayan da majalisar Kansiloli ta Shira a ranar 3 ga watan Maris ta cire shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Abdullahi Ibrahim Beli, da mataimakinsa, Hon. Usman Adamu.
Shugaba da mataimakinsa an tsige su ne kan zargin almundahana, rashin ɗa’a, rashin mayar da hankali kan aiki da kuma cin zarafin ofisoshinsu.
Kafin masa wannan naɗin riƙon kwarya, Wali ya kasance Kansila da ke wakiltar gundumar Tumfafi kuma shi ne ya kasance shugaban Kansiloli na ƙaramar hukumar.
Gwamnatin jihar Bauchi ce ta sanar da rasuwar nasa a ranar Lahadi ta cikin sanarwar manema labarai da kakakin gwamnan jihar, Mukhtar Gidado, ya fitar.
Da ya ke miƙa ta’aziyyasa ga iyalan mamacin, gwamna Bala Muhammad ya misalta marigayin a matsayin jajirtaccen mutumin da ya hidimta wa jama’a tare da bayar da gudunmawarsa wajen kawo cigaba a ƙaramar hukumar Shira da ma jihar Bauchi.
Gwamnan ya yi addu’ar Allah jiƙan mamacin ya gafarta masa kura-kuransa tare da neman Allah ya bai wa iyalai haƙurin juriya.
Rasuwar Wali dai na zuwa ne kwanaki 13 kacal a gudanar da zaɓen cire girbi na wanda zai bayar da dama a zaɓi sabon shugaba da mataimakinsa na karamar hukumar Shira.
Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Bauchi (BASIEC), Mr. Ahmed Makama, ya shaida wa ‘yan jarida cewa dukkanin shirye-shiryen da suka dace na gudanar da zaɓen cike girbi a ranar 24 ga watan Mayun 2025 ya kammala.
BASIEC dai tun da farko ta gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi na jihar ne a watan Agustan 2024, inda aka zaɓi shugabanni da mataimakansu a dukkanin faɗin ƙananan hukumomi 20 da suke jihar Bauchi.
Makama ya bada tabbacin gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe mai cike da adalci.
Ya sanar da cewa kuɗin fom na kujerar shugaban ƙaramar hukumar Shira Naira miliyan 1, yayin da na mataimaki ya kasance Naira dubu ɗari biyar. Ya nemi dukkanin masu sha’awar tsayawa takarar da su fito su fara nema domin ƙofa a buɗe take.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp