A kwanan nan ne sakatare janar na kungiyar ASEAN Kao Kim Hourn ya bayyana a wata hirar da ya yi da wakilin babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG cewa, nasarorin da Sin ta samu ta fuskar ci gaba ba sakamakon ‘siddabaru’ ba ne, illa sakamakon aiki tukuru kuma mai dorewa.
Kao Kim Hourn, wanda ya ziyarci kasar Sin sau da dama, ya yi tsokaci kan abubuwan da ya gani a wadannan ziyarce-ziyarcensa. Ya bayyana cewa, tafiya daga filin jirgin sama zuwa tsakiyar gari, ya shaida yadda kasar Sin take da tsabta, da koren muhalli, da tsaro, da duk sakamakon ci gabanta na zahiri. Abin ban mamaki ne ganin yadda kasar Sin ta canza a cikin ‘yan shekarun nan. Abubuwan da ya gani a kasar Sin a cikin ‘yan shekarun nan sun matukar bambanta da abubuwan da ya gani lokacin da ya ziyarci kasar Sin a shekarun 1990.
Ya jaddada cewa, irin wadannan sauye-sauyen na nuna gagarumin kokari na bayan fage. Kana samun ci gaba yana bukatar aiki tukuru. Kao ya bayyana cewa, ci gaban da kasar Sin ta samu ne ba ta hanyar siddabaru ba, ta samu ne a sakamakon namijin kokarin da shugabannin kasar Sin da jama’arta suka yi. Ya kuma kara da cewa, ci gaban kasa yana bukatar kuzari mai yawa, da nagartaccen jagoranci, da dimbin albarkatu, da jajircewar al’ummarta. Kasar Sin misali ce ga hakan. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp