… ci gaba daga makon jiya
5. Kin zama wacce ba ta son ci gaba ba?
Idan mace ba ta da ilimi ko wayewa a kan yadda za ta kula da mijinta da gidanta, tana zama abin dariya a wurin miji. Hakan kan sa ya fara kallon ta da raini. Wannan kuskure ne da ake nadama sosai daga baya.
6. Rashin iya magana
Maganar mace tana iya gina aure ko rusa shi. Idan kika yi amfani da harshenki wajen zagi, tsinuwa, da cin zarafi, kin riga kin fara gina bango tsakaninki da mijinki. Kuma wannan kuskure ne da ake yin kuka a kai daga baya.
7. Barin kanki ba kula da kanki
Mace da ta daina kula da tsafta, kamshi, da kwalliya a cikin gida tana sa mijinta ya fara daina ganin armashinta, ki kula, mijinki zai iya samun abin da ke burge shi a waje, amma bai kamata ya rasa hakan a wurinki ba. Wannan babban kuskure ne da za ki yi nadama idan kika yi sakaci.
8. Rashin zama mai hakuri
Aure ba kyakkyawa ba ne kadai, akwai gwaji, akwai jarabawa. Idan mace ba ta da hakuri, tana iya ruguza gidan aurenta da kanta. Hakuri shi ne kashin bayan nasarar kowanne aure.
9. Kin sanin darajar mijin ki
Idan kika daina nuna masa cewa ke kina godiya da shi, kina ganin komai ya zama dole, to kin fara ruguzawa. Miji yana bukatar a yaba masa, a nuna masa daraja. Idan kika yi sakaci, sai ya fara neman inda zai sami hakan.
10. Kin guje wa shawarar Allah
Dukkan kuskuren da aka ambata a sama ya samo asali daga barin koyarwar addini. Idan mace ta tsaya da gaskiya, ta kiyaye umarnin Allah da na Manzonsa, ba za ta aikata wadannan kurakurai ba. Amma idan ta bar su, aure na zama cike da nadama da bakin ciki.
Karshen magana:
Kuskure a aure na iya zama karami a idon mace, amma yana iya zama babban abu da zai rusa ginin da ta dauki shekaru tana ginawa. Kada ki bari wata rana ki ce “Da na sani.” Saboda lokacin da kalmar nan ta fito, lallai nadama ta riga ta mamaye zuciyarki.
Ki tsaya, ki gyara, ki kasance mace ta daban mace mai daraja a idon mijinta.