Babban mai tsawatarwa na majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume, ya yi zargin cewa, wasu ministoci ba sa iya ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu domin tattaunawa kan illar tsadar rayuwa da karancin abinci a Nijeriya.
Idan dai za a iya tunawa, Sanata Ndume, tare da takwaransa, Sunday Karimi, a ranar Talata ne suka dauki nauyin wani kudiri na neman gwamnati ta sanya dokar ta baci kan matsalar karancin abinci a Nijeriya.
- Nan Ba Da Jimawa Ba Makiyaya Za Su Ci Gaba Da Jigilar Dabobbi A Jirgin Kasa – NRC
- Majalisa Zata Miƙawa Shugaban Ƙasa Ƙudurin Dokar Kafa Hukumar Cigaban Arewa Maso Yamma
Sun daura alhakin kiran na su kan gargadin da hukumar samar da abinci ta duniya ta yi, inda ta yi hasashen cewa ‘yan Nijeriya miliyan 82 za su fuskanci karancin abinci a cikin shekaru biyar masu zuwa.
Da yake zantawa da BBC Hausa jim kadan bayan kammala zaman, Ndume ya ce gazawar gwamnatin tarayya na magance wadannan matsalolin babban kalubale ne.
Ya ce: “Babbar matsalar da ke tattare da wannan gwamnati ita ce, kofofinta a rufe suke ta yadda har wasu ministoci ba za su iya ganin shugaban kasa ba, balle ‘yan majalisar dokokin kasar, wadanda ba su da damar ganawa da shi, su tattauna batun. al’amuran da suka shafi mazabarsu.”