Wasu daga cikin kungiyoyi masu zaman kansu a Nijeriya sun nuna damuwarsu kan cewa zai yi wuya Hukumar zabe ta kasa INEC ta iya yi wa ‘yan kasar da ke son yin katin zabe rijista, saboda rashin wadatattun kayan aikin.
Kungiyoyin dai sun ce hukumar zaben kasar na da karancin wadatattun ma’aikatan da suka kamata wajen yi wa ‘yan kasar rijista, da kalubalen da ke tattare da na’urorin da ake amfani da su wajen yin rijistar.
Jihar Kano na daga cikin jihohi a Nijeriya da ake da karancin wadanda ba su fito yin katin zaben ba, inda kungiyoyin su suka alakanta hakan da gajen hakurin wadanda suka yi rijista zuwa ofishin hukumar zabe don a dauki bayanansu. Inji BBC Hausa.