Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi la’akari da irin wahalhalun da talakawan Nijeriya ke fuskanta a sakamakon sauay fasalin kudin kasar nan suka yi.
Gwamnan ya ce wahalhalun da ake fama da su a yanzu suna da yawa, ya kuma yi kira gare shi da ya yi biyayya ga hukuncin da kotun koli ta yanke.
- Kotu Ta Yanke Wa Mutum 2 Hukunci Kisa Kan Kashe Ma’aurata A Ondo
- Na Bai Wa Bankuna Umarnin Wadata Mutane Da Takardun N200 – Emefiele
Soludo, wanda ya yi jawabin a yayin bikin jana’izar Ministan Sufurin Jiragen Sama na Jamhuriya ta farko, Cif Mbazulike Amechi, ya bayyana cewa: “Ina mika godiya ga shugaban kasa kuma kwamanda a tarayyar Nijeriya, Muhammadu Buhari, Cif Chris Ngige ya wakilta.
“Ina kira ga shugaban kasa da ya yi la’akari da irin radadin da al’ummar Nijeriya ke fuskanta sakamakon sauya fasalin Naira.
“Tunda Kotun Koli ta bayyana cewa tsohon da sabbin takardun Naira su ci gaba da aiki har sai an yanke hukunci, ya kamata shugaban kasa ya yi biyayya ga hukuncin kotun koli, wanda ya tabbatar da shi a matsayin Shugaban Nijeriya.”