Duk da cewa ana samun kudade aBankuna da wuraren cire kudade, amma duk da akwai karancin su ahannun jama’a wanda hakan ke cigaba da barazana ga harkokin kasuwancin jihar Kano daman a kasa baki daya.
Bayani haka ya fito ne daga bakin wani dankasuwa dake kasuwar kantin kwari dake Kano, Alhaji Muhammad Sakir Daurawa, alokacin da yake zanatwa da manema labarai.
- Tsakanin Samari Da ‘Yan Mata, Wa Ya Kamata Ya Ba Wani ‘Ramadan Basket’
- Dan Takarar NNPP Ya Kayar Da Dan Majalisa Mai Ci A Fagge
Muhammad Sakir Daurawa, ya ce duk wannan barazana ana samun ciniki , amma yana da kyau gwamnati ta duba wannan lamarin da kyau domin daukar matakin daya dace musamman kudi su wadata ahannun jama’a idan gwamnatin ta yi haka zai bunkasa tattalin arzikin jihar Kano da kasa baki daya.
Takaita kudi a hannun jama’a kasashen da suka cigaba su suke irin wannan saboda muna karain cigaba .Daurawa ya I amfani da wannan dama da taya al’ummar musulmin jihar murnar lafiya.