A yayin da hauhawar farashi ke karuwa, karancin samun kudaden shiga ga masu sana’a ya jefa a kalla ‘yan Nijeriya miliyan 14 cikin kangin talauci da fatara a shekarar 2024.
Wannan bayanin na kunshi ne cikin rahoton Babban Bankin Duniya kan yanayin talaucin da ke faruwa a kasashe.
- Manyan Kugiyoyin Gasar Firimiya Sun Fara Zawarcin Victor Osimhen
- Sin Ta Harba Kumbon Tianzhou-8 Na Dakon Kayayyaki Zuwa Tashar Binciken Samaniya Ta Tiangong
A cewar rahoto, kaso 47 na ‘yan Nijeriya a halin yanzu suna rayuwa ne cikin rukunin talakawan duniya na layin dala 2.15 a rana guda, yayin da hauhawa da buga-bugan neman tattalin arziki suka kasace cimma bukatun da suke akwai na ci gaban jama’a.
A matakin tunkarar talaucin da ke karuwa, a cewar rahoton, gwamnatin Nijeriya ta kaddamar da shirin tallafin kudi na wucin-gadi da nufin taimaka wa magidanta miliyan 15.
Kowani magidanci zai amshi naira 75,000, da za a ba su a matakin sau uku, wadanda za su amfana ana kiyasin mutum miliyan 67.
Babban bankin duniyan ya ce, ana harsashen talaucin ka iya zuwa kaso 52 a nan da shekarar 2026, don haka akwai bukatar gwamnatin Nijeriya ta tashi tsaye wajen bijiro da shirye-shiryen da za su kawo sauki da cero jama’a daga cikin wannan yanayin na talauci.
Domin magance matsalar hauhawar farashin kayayyaki, Babban Bankin Nijeriya ya daga darajar hada-hadar kudade zuwa maki 850 daga watan Fabrairu zuwa Satumban 2024, tare da kara yawan kudaden ajiya.