Hukumar tsaron farin kaya ta Nijeriya, (NSCDC), ta yi gargadi game da karkatar da man fetur da kuma boye man fetur din.
Kwamandan hukumar na Jihar Jigawa, CC. Musa A Malla ne, ya yi wannan gargadin ne a ranar Talata a wajen bikin sabbin jami’ai 66 da aka yi wa karin girma wanda ya gudanar a hedikwatar rundunar da ke Dutse.
- Dabarar Da Kasar Sin Ta Dauka Wajen Zamanintar Da Al’umma
- Sojoji Sun Cafke Mutum 40 Masu Yi Wa ‘Yan Ta’adda Safarar Kayan Abinci
Ya ce rundunar ‘yansandan jihar tana kokarin duba yadda ake karkatar da motocin man fetur a fadin jihar da ma kasa baki daya.
“Dakarunmu suna sanya ido kan ayyukan gidajen mai domin kawo karshen karancin man fetur da ake fama da shi a jihar,” in ji shi.
Malla ya ce rundunar ba za ta nade hannayenta ba, ta bai wa ‘yan kasuwa da gidajen mai su jawo wa ‘yan kasa wahala da ba dole ba.
Sai dai ya bukaci wadanda aka yi wa karin matsayi da su dauke shi a matsayin wani kalubale na kara yawan aiki.
“Wanda aka yi wa karin girma ana sa ran zaku kara yin aiki tukuru don mayar don cimma nasara” in ji CC Malla.