Tun bayan da gwamnatin Amurka ta bayyana kakaba sabbin harajin fito da ta kira na “Ramuwar Gayya” a farkon watan nan, masharhanta ke ta bayyana baike, da sukar lamarin wannan mataki, suna masu bayyana shi a matsayin yakin cinikayya da ba abun da zai haifar sai koma baya ga ita kanta Amurka da ma kasashen duniya a matakai daban daban.
An riga an ga hakan a zahiri, yayin da Amurka ta kakaba kaso 125 bisa dari kan hajojin kasar Sin da ake shigarwa kasar, nan take matakin ya jefa kasuwannin hannayen jarin kasa da kasa cikin halin rashin tabbas. Kazalika, darajar hannayen jarin kamfanoni daban daban suka rika karyewa biyo bayan hakan.
- Shugaba Xi Ya Jaddada Aniyar Kasarsa Ta Goyon Bayan Kudurorin Kyautata Yanayi Da Ci Gaba Marar Gurbata Muhalli
- Harin Lakurawa: Shugaban Karamar Hukuma Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Sokoto
Domin kare matsayarta, gwamnatin Amurka ta ce matakin kakaba harajin ya samar mata da dama ta rage gibin ribar cinikayya, da farfado da masana’antun cikin gida, da cika aljihun gwamnatin da kudaden haraji. To, amma abun tambayar shi ne wannan magana haka take? Amsar dai a bayyane take, domin kuwa dukkanin masana tattalin arziki na cewa gibin cinikayya da Amurka ke fama da shi ba wai ya faru ne daga goyayyar kasuwannin waje ba, maimakon haka matsala ce dake da alaka da manufofin tattalin arzikin kasar marasa inganci. A halin da ake ciki tattalin arzikin Amurka na kara karkata ga fannonin hada-hadar kudade da sarrafa kayan fasahohi da sauransu, yayin da fannin sarrafa hajojin amfanin yau da kullum ke can a baya, wanda hakan ya sa ala tilas kasar ta dogara ga hajojin da ake shigarwa kasar daga kasashen waje.
Bugu da kari, masharhanta da dama na ganin karin harajin fito ba zai warware matsalar da Amurkan ke ciki ba. Ko shakka babu idan Amurka na son ta tunkari wannan kalubale bisa gaskiya, sai ta sauya tsarin ilimi, ta kuma bunkasa fannin kirkire-kirkirenta, da daga martabar masana’antu, da zuba jari na dogon lokaci a fannin, ba wai matakin jeka-na-yika na gajeren lokaci, irin wannan na baiwa kasuwa kariyar cinikayya ba.
A daya hannun kuma baya ga illar da wannan kare-karen haraji ya haifar, matakan kasashen da lamarin ya shafa na ramuwar gayya na iya haifar da hauhawar farashi na gaggawa, da jefa tattalin arzikin sassa daban daban cikin halin komada, a maimakon fatan da gwamnatin Amurkan ke yi na sake mayar da kasar “Zakaran gwajin dafi.” (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp