Karin farashin man fetur na baya-bayan nan ya yi matukar ta da hankalin ‘yan kasuwar mai da kamfanin mai na kasa tare da kungiyar masu sayar da man fetur mai zaman kanta inda (IPMAN) din da gana da kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) kan sabon gyaran farashin man fetur.
Shugaban Kungiyar IPMAN, Abubakar Maigandi, ya bukaci hukumar ta NNPC da ta sayar da man fetur ga mambobinta bisa ga farashin da matatar man Dangote ta ba ta.
- MOFA: Ministan Harkokin Wajen Birtaniya Zai Ziyarci Kasar Sin
- Mambobin Kungiyar SCO Sun Bayyana Adawa Da Matakan Kariyar Cinikayya
Yayin da yake magana a jiya a gidan Talabijin na Channels, Maigandi, ya kuma bukaci a mayar musu da kudaden da ‘yan kasuwar man ke bin su, wadanda ya ce hukumar ta NNPCPL ta rike tun watanni uku da suka gabata. Hakan ya zo ne sa’o’i 24 bayan da kamfanin NNPC ya yi karin farashin man fetur.
Kamfanin mai na kasa ya daga farashin man zuwa N1,030 daga N897/litta a Abuja, sannan ya karu zuwa Naira 998 daga Naira 868 a Legas.
Sauran wuraren dai an samu hauhawar farashin kaya, inda miliyoyin ‘yan Nijeriya ke korafin cewa an jefa su cikin mawuyacin hali.
Shugaban na IPMAN ya jaddada matsalar kudi ce da aka rikewa ‘yan kasuwar man fetur, inda ya bukaci hukumar NNPC da ta dauki matakin gaggawa wajen ganin an daidaita lamarin.
Babban kalubalen da muke fuskanta a yanzu shi ne, muna da bashin da ake bin kamfanin na NNPC da kamfanin ya tara kaya ta hanyar matatar Dangote a farashi mai rahusa. Yanzu haka, kudinmu yana tare da su (NNPCL) kusan watanni uku”, in ji shi
Shima da yake zantawa da Sashen Hausa na BBC, shugaban kungiyar IPMAN a yankin Arewa, Alhaji Salisu Tantan, ya ce kamfanin NNPC ya sayi kayan a kan Naira 898 kan kowace lita daga matatar Dangote amma yana sayarwa da sama da Naira 1,000.
“Mun yi matukar kaduwa da cewa (NNPCL) sun sayar mana da shi fiye da yadda muke tsammani,” in ji shi.
Ya ce a halin yanzu ba abu ne mai wuya su sayar wa jama’a kayan a kan farashi mai rahusa ba, la’akari da cewa dole ne su dauki nauyin sufuri.
Da aka tambaye shi dalilin da ya sa suka kasa dauke kayan kai tsaye daga matatar Dangote, jigon na IPMAN ya ce suna yin iya kokarinsu don cimma wannan matsayar.
“Akwai tsari na musamman tsakanin NNPC da Dangote; suna ba shi danyen mai; ya kuma biya su a Naira. Zai yi mana wuya mu shiga cikin irin wannan tsari cikin sauki,” in ji shi.
Farashin zai sauko – cewar sashen kasuwanci na NNPCL
Sai dai wani jami’in kamfanin NNPC a daren jiya ya kare matakin da suka dauka, inda ya ce karin da aka yi a baya-bayan nan ya shafi kasuwar man fetur ta duniya da kuma canjin Naira da Dala.
Malam Lawan Sade, wanda shi ne Manajan Darakta na Kamfanin Trading na NNPCL, ya shaida wa BBC cewa farashin man fetur ya yi yawa sosai, musamman idan matatun mai da gwamnati ke gyarawa suka shigo cikin tsarin.
Sade ya ce farashin man fetur ya yi dai-dai da bukatun duniya, kuma a matsayinsa na kamfani mai zaman kansa, kamfanin na NNPC yana mayar da martani ga sauye-sauyen bukatu da wadata.
“Muna kira ga ‘yan Najeriya da su yi hakuri da mu. Za a daidai lamarin domin samar da fa’ida cikin lokaci,” in ji shi.
IPMAN na fatan samun saukin farashi bayan da aka fara tattaunawa da Dangote
An ruwaito cewa ‘yan kasuwar masu zaman kansu sun fara tattaunawa da hukumar gudanarwa ta Dangote biyo bayan tsoma bakin hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da hukumar kula da harkokin man fetur ta kasa (NMDPRA).
A karshe dai kungiyar IPMAN ta bayyana wa kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL) cewa farashin man da take samu daga kamfanin mai na kasa ya haura Naira 898 akan kowacce lita yadda suke saya daga Dangote.
A cewar shugabanta kungiyar na kasa, Abubakar Maigandi, kamfanin na NNPC ya rike da kimanin Naira biliyan 15 na ‘yan kasuwa masu zaman kansu tsawon watanni uku da suka gabata.Sai dai wata majiya daga IPMAN da ta zanta da wakilinmu a jiya ta ce hukumar ta NNPC ta amince da bai wa IPMAN damar sayan man kai tsaye daga Dangote.
Hakan ya biyo bayan matakin da kamfanin mai na kasa ya dauka na barin matsakaita masu daukar mai wajen rabon mai daga matatar mai girman 650,000.
Gwamnatin tarayya ta bayyana a karshen makon da ya gabata cewa, a yanzu ‘yan kasuwar man sun samu ‘yancin yin shawarwarin sayen man fetur kai tsaye daga matatar Dangote ba tare da neman izinin hukumar ta NPL ba.
Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun wanda ya bayyana hakan ya ce, “A ci gaban da aka samu, ‘yan kasuwar man fetur sun samu damar sayan kayan kai tsaye daga matatun mai na cikin gida ba tare da aikin shiga tsakanin na NNPC ba. Ana karfafawa gwiwar ’yan kasuwa da su fara sayayya kai tsaye daga matatun mai bisa sharudan kasuwanci da aka yi sulhu tsakanin juna, wanda zai habaka gasa da habaka ingantaccen kasuwaci.
A makon da ya gabata ne kamfanin NNPC, wanda shi ne na daya a kasuwa a kasar, ya daidaita farashin famfo, inda ya kara daga Naira 855 zuwa Naira 998 kan kowace lita a Legas da kuma sama da Naira 1000 a wasu jihohi.
SERAP ta bukaci Tinubu da ya janye sabon farashin mai
Kungiyar Kare Hakkokin Tattalin Arziki (SERAP) ta yi kira ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da ya janye sabon farashin man fetur na baya-bayan nan har zuwa lokacin da za a yanke hukuncin karar da ta shigar gaban babbar kotun tarayya da ke Legas wadda take kalubalantar ikon kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL) kan kara farashin man.
SERAP ta nanata cewa idan aka bar wannan karin na baya-bayan nan ya tsaya, to zai zama abin izgili ga shari’ar da ke gaban kotu, wanda hakan zai haifar da hatsarin da zai kawo cikas ga shari’ar ko kuma a nuna son zuciya, kamar yadda ake yi.
Kungiyar ta yi wannan ikirari ne a wata budaddiyar wasika mai kwanan watan 12 ga watan Oktoba 2024 dake dauke da sa hannun mataimakin daraktan SERAP Kolawole Oluwadare, cewa daya daga cikin muhimman ka’idojin da doka ta tanada ita ce ta shafi kowa da kowa, ciki har da shugabanni da hukumomin gwamnati.
SERAP ta ci gaba da cewa, barin babbar kotun tarayya ta saurari shari’ar da kuma yanke hukunci zai yi daidai da ka’ida da tsarin mulkin Nijeriya na (da aka yi masa gyara a 1999), kan rantsuwar da kuka yi da kuma alkawurran da kuka sha na tabbatar da doka.
A watan da ya gabata ne dai kungiyar farar hula ta maka gwamnati da kamfanin na NNPC gaban kotu domin kalubalantar halaccin karin farashin man fetur da kuma rashin binciken zargin cin hanci da rashawa a hukumar ta NNPC.
Ra’ayoyin jama’a game da sabon farashin mai
An ci gaba da mayar da martani dangane da karin farashin man fetur da kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPC) ya yi.
Karin farashin man fetur ya tayar da hankulan jama’a a baya-bayan nan, inda yanzu ya kai Naira 1,030 kan kowace lita a Abuja da kuma Naira 998 a Legas. Wannan shi ne karo na biyu da aka kara kudin mai cikin wata guda, wanda ke nuna hauhawar kashi 430 cikin 100 tun daga watan Mayun 2023.
Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa, masana’antu, ma’adinai da noma ta Nijeriya (NACCIMA), Dele Kelbin Oye, ya nuna damuwarsa kan karin farashin man.
Da yake mayar da martani kan hakan, Oye ya ce: “Sabon karin farashin man zuwa Naira 998 kowace lita a Legas da kuma Naira 1030 a Abuja na da matukar tasiri ga kasuwanci da gidaje a Nijeriya.
Har ila yau, Kungiyar ‘Yan Kasuwa (TUC) ta bukaci gwamnatin tarayya da ta aiwatar da wani shiri na musamman na musayar kudaden waje ga matatar Dangote domin daidaitawa da rage farashin man fetur.
Shugaban TUC, Festus Osifo a wani taron tattaunawa da aka yi jiya a Abuja, ya bayyana cewa, rage ka’idojin da aka samu a bangaren man fetur, tare da sauye-sauyen canjin kudi ne, ya haifar da hauhawar farashin mai, inda farashin ya haura Naira 1,000 kan kowace lita.