Gwamnatin jihar Kebbi ta amince da ware Naira miliyan 1 ga kowane mahajjaci daga cikin 3,344 da ke da niyyar zuwa aikin Hajjin bana daga jihar don kammala biyan karin kudin aikin da hukumar aikin hajji ta kasa, NAHCON ta yi.
An cimma wannan matsaya ne a taron majalisar zartarwa na gaggawa wanda mataimakin gwamnan jihar, Sanata Umar Abubakar Tafida ya jagoranta a Birnin Kebbi a ranar Litinin.
- Gwamnatin Kebbi Ta Amince Da Murabus Din Babban Limamin Masallacin Wala
- An Dakatar Da Shugabar Matan APC A Kaduna Kan Sukar Uba Sani
Da yake karin haske ga manema labarai game da sakamakon taron, kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar, Alhaji Yakubu Ahmad Birnin Kebbi, ya ce sun dauki wannan mataki ne domin kara daukaka martabar Gwamna Nasir Idris na ganin an kiyaye dabi’un addini domin zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’umma.
“A cikin kimanin Naira miliyan 2 da NAHCON ta nema a matsayin karin kudin tafiya, gwamnatin jihar Kebbi ta tallafawa kowane mahajjaci da Naira miliyan 1.
“Alhazan da suka kammala biyan kudin tafiya suma za su ci gajiyar Naira miliyan 1 daga gwamnati,” in ji Kwamishinan.