Rahotanni na cewa, a shekarar 2024 da ta gabata, gwamnatin kasar Sin ta fadada hadin gwiwa a fannonin binciken kimiyya da fasaha, inda ta shiga yarjeniyoyin hadin gwiwa har 118, da wasu gwamnatocin kasashen waje, tare da gina dakunan gwaje-gwaje sama da 70, karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, an kuma samu sakamako mai gamsarwa a manyan ayyuka, da shirye-shiryen binciken kimiyya na kasa da kasa.
A halin da ake ciki, Sin ta aiwatar da muhimman matakai na zama babbar cibiyar binciken kimiyya da fasaha, inda adadin kudaden da ta kashe a fannonin bincike, ya kai matsayi na biyu a duniya, yayin da jimillar jami’ai masu aiki a fannin, da adadin neman rajistar kariyar ikon mallakar fasaha na kasa da kasa na kasar Sin, ya kai matsayi na farko a duniya a cikin shekarun baya-bayan nan.
- Xi Ya Zanta Da Babban Jagoran Vietnam Da Shugaban Sri Lanka
- ‘Yan Bindiga Sun Koma Neja Bayan Sulhu Da Gwamnatin Kaduna
Har ila yau, Sin na kan gaba a adadin nasarorin da aka cimma, a fannin kirar abubuwan harhada na’urorin laturoni na IC, da kirkirarriyar basira ko AI, da fasahar tattara bayanai ta “quantum”, da sauran karin wasu fannoni.
Bugu da kari, kasar Sin ta zamo a sahun gaba wajen cin gajiyar kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, dake tallafawa bunkasar tattalin arziki da zamantakewar al’umma. Yayin da kuma kasar ke matsayi na 11 a jerin kasashen dake kan gaba, a alkaluman awon kwarewa a fannin kirkire-kirkire. (Saminu Alhassan)