Wani yunkuri da gwamnatin tarayya ke yi na dakile yunkurin tsunduma yajin yakin sai Baba-ta-gani da kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC) ke shirin yi, ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong, ya bayyana fatansa da kwarin guiwarsa na ganin an warware matsalolin bayan wata muhimmiyar ganawa da mataimakin shugaban kasa, Kasshim Shettima.
Da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin tarayya bayan ganawar a ranar Laraba, Lalong ya jaddada kudirin gwamnati na kyautata jin dadi da walwalar ma’aikatan Nijeriya.
Ya ce, “Mun samu cikakken lokaci na tattaunawa tare da kungiyar kwadago ta Nijeriya, Babban burin shugaban kasa shi ne, inganta walwala da wadata ma’aikata. Ba bu kokwanto.”
Lokacin da aka tambaye shi game da barazanar yajin aikin da kungiyoyin kwadago suka yi, Lalong ya ba da tabbacin cewa, “Kada ku damu da hakan. Shi ya sa na ce tsakanin mu da NLC akwai zumunci mai karfi a tare da mu. Ba mu da wata fargaba game da wasu abubuwan da suka gabatar da kuma shawarwari da kuma kunshin romo da gwamnatin tarayya ta tanada.”
A nasa bangaren, sakataren gwamnatin tarayya (SGF), George Akume, ya bayyana kwarin guiwar cewa, shugabannin kwadagon, suna fatan kyautata rayuwar al’umma kuma suna kishin Nijeriya, don haka, zai yi wuya su tsunduma yajin aikin.
Akume ya jaddada kudirin gwamnati na inganta yanayin rayuwa ga daukacin ‘yan Nijeriya da samar da wadata.