Babban rukunin gidan rediyo da talibijin na kasar Sin CMG, ya sanar a jiya Lahadi a nan birnin Beijing cewa, a karon farko zai watsa shirye-shiryen shagalin murnar sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta kasar Sin ga mutane masu bukata ta musamman.
A gun taron manema labarai da aka yi a wannan rana, jami’in CMG ya ce, ’yan wasa masu magana da hannu za su yi amfani da fasaha ta zamani ciki hadda AI, don karfafa kwarewarsu a bangaren magana da hannu da gabatar da bayanai don taimakawa kurame wajen shakatawa da shirye-shiryen da za a gabatar a yayin shagalin. Kazalika, za a gabatar wa makafi karin bayani kan shirye-shiryen shagalin. (Amina Xu)