Ma’aikatan Jihar Kano, sun jinjina wa Gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa karramawar da ya samu na “Gwamnan Da Yafi Tausaya wa Ma’aikata” wanda Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC), reshen Kano, ta bayar.
A cikin saƙon taya murna da ya sanya wa hannu, Shugaban Ma’aikatan Jihar Kano, Abdullahi Musa, ya yaba wa gwamnan kan muhimman sauye-sauyen da ya kawo da suka inganta jin daɗin ma’aikatan jihar.
- Zanga-zangar Yunwa: ‘Yansanda Sun Buƙaci Amnesty Ta Janye Zargin Tauye Haƙƙi
- Saurayi Ya Fille Kan Budurwarsa A Nasarawa
Daga cikin nasarorin gwamnan akwai ƙara kuɗin fansho daga Naira 5,000 zuwa Naira 20,000, shigar da ma’aikata 10,000 da aka ɗauka a baya cikin sahun aikin gwamnati.
Sauran sun haɗa da ɗaukar sabbin ma’aikatan lafiya, malamai, da jami’an tsaro.
Bugu da ƙari, Gwamna Abba ya amince da sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 71,000, wanda ya zarce na gwamnatin tarayya.
Haka kuma, gwamnatinsa ta yi adalci wajen naɗin sakatarorin dindindin, inda aka daina yin siyasa a naɗin.
Gwamnan ya kuma biya bashin fansho sama da Naira biliyan 16, tare da tabbatar da biyan albashi da fansho a kan lokaci, wanda ya tabbatar da amincin gwamnatin wajen sarrafa kudaden jama’a.
Gwamnan ya mayar da hankali wajen horarwa da sake fasalin ma’aikatan gwamnati don ƙara musu ƙwarewa da inganta ayyukansu.
Ta hanyar shirye-shiryen horarwa da kyautata yanayin aiki, gwamnatinsa ta shimfiɗa tubalin ci gaba mai ɗorewa da inganta shugabanci.
An kuma yi kira ga ma’aikata su ci gaba da himma wajen gudanar da ayyukansu, domin ci gaban Jihar Kano.
Karramawar da NLC ta yi wa Gwamna Abba ba kawai yabo ba ne, alama ce ta haɗin kan gwamnati da ma’aikata wajen kawo ci gaba mai amfani.