Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa samun lambar yabo ta “Gwamna Mafi Nagarta Na Shekara” daga jaridar LEADERSHIP babban ƙarfafawa ce gare shi domin ci gaba da gudanar da ayyuka masu tasiri ga al’ummar jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi takardar sanarwar kyautar daga tawagar kamfanin jaridun LEADERSHIP ƙarƙashin jagorancin Babban Editan jaridar, Azu Ishiekwene, a birnin Abuja.
- Sanata Barau Zai Yi Ƙarar Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10
- Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC
Gwamna Lawal ya ce, “Wannan lambar yabo ta ƙarfafa ni sosai. Tana nuna cewa mutane suna lura da abin da muke yi, kuma za mu ci gaba da ƙoƙari don tabbatar da cewa canjin da muke son kawo wa Zamfara ya tabbata. Ina matuƙar godiya, domin wannan yabo shaida ce ta abin da muka cimma cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.”
Ya ƙara da cewax gwamnatinsa ta fara gyara daga tushe, inda ilimi ya zama ginshiƙin farko. “Shekaru takwas kafin mu hau mulki, ɗalibanmu ba su samun takardun WAEC, sannan tsawon shekaru biyu suna fama da matsalar NECO. Na biya Naira Biliyan huɗu don magance wannan matsala,” inji shi.
Gwamnan ya bayyana irin matsalolin da ya gada, yana mai cewa: “Na samu asusun gwamnati da naira miliyan huɗu kacal. Ma’aikata suna karɓar albashi cikin rashin tabbas, babu ruwa, asibitoci kuwa suna cikin mummunan yanayi.”
Lawal ya ce, ya sake fasalin tsarin gwamnati, inda ya rage yawan kwamishinoni da manyan sakatarorin don rage ɓarna da ƙara inganci. “Yanzu muna daga cikin jihohi mafi ci gaba wajen tara haraji, inda kuɗaɗen shiga suka ƙaru da fiye da kaso 300 cikin 100,” inji shi.
Ya bayyana cewa gwamnatin sa ta gina ko ta gyara makarantu sama da 500, tare da aiwatar da ayyukan da kuɗinsu ya kai biliyan N10 a kowace ƙaramar hukuma. Duk da cewa ana cire biliyan 1.2 a kowane wata daga kuɗaɗen gwamnati don biyan basussuka, an biya bashin fansho da giratuti na fiye da biliyan N13.6 da aka tara tun shekarar 2011.
A ɓangaren tsaro, Lawal ya ce jihar ta ɗan sami sauƙi bayan kafa rundunar tsaron gida, yayin da gwamnati ke ƙoƙarin tabbatar da amfanin mulki ya kai ga talaka.
A nasa jawabin, Babban Editan LEADERSHIP, Azu Ishiekwene, ya ce an bai wa gwamnan wannan lambar yabo ne saboda irin nasarorin da ya samu a fannonin tsaro, ilimi, lafiya da gine-gine, yana mai cewa “jarida tana da alhakin duba gwamnati, amma kuma tana da haƙƙin yabawa idan ana yin daidai.”














