Ma’aikatar raya al’adu da yawon bude ido ta kasar Sin ta yi kiyasin Sinawa sun yi tafiye-tafiye miliyan 314 yayin hutun ma’aikata da aka yi tsakanin ranar 1 zuwa 5 ga watan Mayu, adadin da ya karu kan na bara da kaso 6.4 bisa dari.
Adadin kudin da aka kashe kan yawon bude ido shi ma ya karu, wanda ya kai yuan biliyan 180.3, kwatankwacin dala biliyan 25, karuwar kaso 8 bisa dari kan na bara, wanda ke bayyana kuzarin kashe kudi tsakanin al’umma.
Hutun na watan Mayu daga 1 zuwa 5, ya kasance daya daga cikin lokutan da aka fi samun tafiye-tafiye a shekara. A lokacin, miliyoyin Sinawa kan yi bulaguro domin ziyartar iyali ko wasu wurare na cikin gida, har ma da kasashen waje. Karuwar tafiye-tafiyen ya kara habaka bangarorin sufuri da na sayar da kayayyaki da na yawon bude ido. (Fa’iza Mustapha)