Wasu abokai sun aiko min sako cewa, BBC ta ba da labaraigame da kasar Sin cewa, tana cin zalun musulmai da tilasta musu aiki a yankin Xinjiang…….Abin bakin ciki ne ganin yadda Intanet ke bunkasa matuka a karni na 21, amma wasu kafofin yada labarai sun zama wani dandali na yada jita-jita da labarai marasa tushe. A hakika, kafofin yada labarai na kasashen yamma sun sha yada irin wadannan karairayi game da kasar Sin da ma sauran wasu kasashe, don neman shafa musu bakin fenti. Hausawa kan ce, ”Gani ya kori ji”, ba za a kai ga gano gaskiya ba, idan an saurari wata kadai ba. Wadannan karairayi da kafofin yada labarai na yamma suke watsawa, sun yi kama da hancin Pinocchio, wani mutum mutumin a cikin almarar kasashen yamma, wanda hancinsa ya yi tsawo saboda karyar da yake bazawa. Ba shakka, Karya fure take ba ta ’ya’ya. (Mai zane: MINA)