Ma’aikatu da hukumomin gwamnati, wadanda ba su gaza 15 ba, ciki har da fadar shugaban kasa da sauran hukumomin da ke hulda da su, sun ware zunzurutun kudi kimanin Naira biliyan 8,997,097,623, domin inganta jin dadi da walwalarsu tare da ware sama Naira biliyan 46 a matsayin na ko-ta-kwana kula da ko-ta-kwana, a cikin kasafin kudi na wannan shekara ta 2024 da muke ciki, kamar yadda binciken LEADERSHIP ya bankado.
Wadannan hukumomi na gwamnati, na tatsar wannan kasafin kudi ta hanyar da ba ta dace ba, duk kuwa da cewa kasar da al’ummar da ke cikinta; musamman wadanda suke a ma’aikatu masu zaman kansu, na shan azabar matsalar tattalin arziki.
- Amurka Na Fakewa Da Guzuma Domin Harbin Karsana
- Bangaren Amurka Ya Mayar Wa Bangaren Sin Da Kayayyakin Tarihi 38 Da Suka Bata Daga Sin
Ofishin kula da kasafin kudi na tarayya, ya samu kaso mafi tsoka na kudade daban-daban, inda aka ware masa zunzurutun kudi har Naira biliyan 920,301,938,040, na ko-ta-kwana ta hanyar amfani da kyakkyawar alaka da Malisar Dokoki ta Kasa, wacce a lokuta da dama ake zargin ta da hada baki wajen kididdiga tare da aiwatar da tsare-tsaren kasafin kudi.
Har ila yau, fadar shugaban kasa kadai, an ware mata Naira biliyan 1,574,940,619; a kasafin kudi na wannan shekara ta 2024.
Kamar yadda kasafin kudin ya bayyana, an ware Naira miliyan 673.17, don jin dadi da walwalar ma’aikatan fadar shugaban kasa. Sai kuma, Naira miliyan 39.83 da aka ware wa ofishin mataimakin shugaban kasa, sannan an ware wa ofishin hulda da gidan gwamnati da ke Jihar Legas Naira miliyan 1.88, haka nan, an ware wa ofishin kula da kadarorin gwamnati Naira miliyan 13.9, inda kuma aka ware wa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFFC), Naira miliyan 104.54.
Sauran wadanda suka ci gajiyar shirin, sun hada da sashen kula da harkokin kudi na Nijeriya (NFIU), inda suka rabauta da samun Naira miliyan 584.88, sai ofishin kula da ba da sautun kayan gwamnati (BPP) da Naira miliyan 100.95, sai Hukumar Kula da Daidaiton Al’amuran Masana’antu ta Nijeriya (NEITI), da Naira miliyan 95.84, yayin da kuma Hukumar Makamashi ta samu Naira miliyan 30. Kazalika; an ware wa Hukumar Bunkasa Filayen Noma ta Kasa Naira miliyan 15, inda aka kuma aka ware wa Hukumar Kula da sauyin yanayi (National Council on Climate Change), Naira miliyan 14.82.
Wato babban abin takaici da ban haushi shi ne, yadda Ma’aikatar Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, wadda ke da alhakin shirya kasafin kudi tare da sanya wa hukumomi ido, ta ware Naira miliya 371,589,777, don kawai ta inganta jin dadin ma’aikatanta. Sai dai kuma, babu wasu gamsassun bayanai game da yadda za a kashe da wadannan kudade, sannan ba a san takamaiman wadanda za su amfana da su ba.
Kodayake, bayanai sun nuna cewa, shelkwatar ma’aikatar; za ta kashe Naira miliyan 185,637,214, wajen jin dadi da kuma walwalar ma’aikata, sai kuma Cibiyar Nazarin Zamantakewa Al’umma ta Nijeriya, karkashin kulawarta za ta amfana da Naira miliyan 50 a nata bangaren na walwala, sannan sai Cibiyar Ci Gaban Gudanarwa ta samu karin Naira miliyan 20. Haka nan kuma, Hukumar Kididdiga ta kasa da ke karkashin ma’aikatar, ana sa ran za ta yi hafzi da Naira miliyan 115,952,563, duk dai don jin dadin ma’aikatan nasu.
Idan wannan abu ya zama abin mamaki, yanzu haka Ma’aikatar Kudi ta Tarayya da wasu hukumomi guda hudu karkashinta, sun kammala shirin kashe zunzurutun kudi har Naira miliyan 655,125,689, don jin dadi da walwalar ma’aikatansu, wanda ya sha ban-ban da albashi da alawus-alawus, ciki har da wasu abubuwa da aka sake maimaita su a cikin kunshin kasafin kudin na bana.
Saboda haka, shelkwatar ma’aikatar ta ware Naira miliyan 180, don jin dadi da walwalar ma’aikatanta, sannan Ofishin Kula da Bashi zai kashe Naira miliyan 15 wajen samar da walwala ga ‘yan tsirarun ma’aikatansa, wadanda za su samu jumillar Naira miliyan 845,131,167 a matsayin albashi daga kasafin kudin kasa.
Haka zalika, ofishin Akanta Janar na Kasa; ya ware Naira miliyan 228,940,407, a matsayin na jin dadi da walwalar ma’aikatansa, wanda za a fitar daga cikin Naira biliyan 3,732,858,625 na kasafin kudin tarayya.
Har wa yau, bayan rage albashin wasu tsirarun ma’aikatantansu da aka yi na kimanin Naira biliyan 2,048,231,918, hukumar ‘yan fansho (PTAD), ta sake ware Naira miliyan 177,517,162 na jin dadi da walwalar ma’aikatansu.
Bugu da kari, bincike ya tabbatar da cewa; Hukumar Tattara Kudaden Shiga da kuma Rabon Kudade (RMAFC), sun ma sun bi wannan sahu na ware makudan kudade na walwala da jin dadi, kimanin Naira miliyan 25,420,000, yayin da Hukumar Biyan Albashi da Tattara Kudaden Shiga ita ke shirin kashe Naira miliyan 28,248,120, a matsayin kudaden walwala da jin dadi. Wani abin mamaki kuma shi ne, Kamfanin Hada-hada da Sayar da Wutar Lantarki; kwata-kwata bai yi yunkurin ware wadannan makudan kudade, don jin dadi da walwala ba.
Ma’aikatar Cikin Gida, na daya daga cikin wadanda suke kan gaba wajen ware wadannan makudan kudade, don walwala da jin dadi, inda nasu kason da aka sahale musu ya kai kimanin Naira biliyan 2,290,896,818, da kuma kari na Naira miliyan 561,298,825 na walwala da jin dadin ma’aikatansu. Babu shakka, wannan dama da aka bai wa Shugabannin Hukumomin Gwamnati, na damar kashe wadannan kudade kai tsaye, zai iya ba su damar karkatar da kudaden ko kuma yin almubazzaranci da su.
Saboda haka, kamar yadda rabon kasafin kudin ya bayyana, Ma’aikatar Cikin Gida; a matsayinta na uwa a cikin jerin wadannan ma’aikatu, za ta samu Naira miliyan 94,392, 582, a matsayin kudaden ko-ta-kwana, yayin da kuma kudaden jin dadi da walwalar ma’aikatanta za su lashe Naira miliyan 35,172,505. Haka nan, a karkashin ma’aikatar; Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), ta samu Naira biliyan 1,075, 259, 358, a matsayin kudaden ko ta kwana (miscellaneous) tare da Naira miliyan 390,330,443, a matsayin na walwala da jin dadi.
A cikin takardar kasafin kudin, Hukumar Tsaro ta NSCDC; za ta kashe Naira miliyan 722,986,563, a matsayin kudaden ko ta kwana, sannan kuma za a batar da Naira miliyan 60,500,000, a matsayin kudaden jin dadi da walwala.
Sa’annan, za a kashe kimanin Naira miliyan 121,060,932, a matsayin ‘yan kudaden kun ji-kun ji da kuma Naira miliyan 14,876, 290, don walwala da jin dadi a Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Kasa.
A bangaren Ofishin Gudanarwar Hukumar Tsaro ta NSCDC, Hukumar Gidajen Gyaran Hali, Hukumar Kashe Gobara da kuma Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (CDCFIB), an ware masa Naira miliyan 17,614,457, sai kuma Naira miliyan 9,842, 857 da aka ware musu a matsayin na walwala da jin dadi.
A halin da ake ciki kuma yanzu, an ware Naira miliyan 259,582,926, a matsayin kudaden ko-ta-kwana, tare kuma da ware Naira miliyan 50, 576,730, a matsayin kudaden jin dadi da walwalar Ma’aikatan Kashe Gobara (FFS).
Ma’aikatar bunkasa Karafuna, ta ware Naira miliyan 62.38; a matsayin kudaden walwala da jin dadi a kasafin kudinta na shekarar 2024. Kasafin kudin ya bayyana Shalkwatar Ma’aikatar Bunkasa Karafuna, a matsayin wadda ta samu Naira miliyan 30, inda Hukumar Binciken Albarkatun Kasa, ta ware Naira miliyan 4.76, haka nan; Cibiyar Bunkasa Karafa ta Kasa, ta ware Naira miliyan 1.416, sannan Cibiyar Horar da Ilimin Karafa, ita ta ware Naira 2.518, sai kuma Hukumar Aikin Hakar Ma’adanai ta Kasa, wacce ita ba ta hakikance ainahin kudaden walwala da jin dadinta ba, amma ta ware Naira miliyan 8.52 a kudaden ko-ta-kwananta.
Sauran kuma, sun hada da Kamfanin Karafa na Ajaokuta, wanda ya ware Naira miliyan 2.16 a matsayin kudaden walwala, yayin da Hukumar Kula da Karafe ta Kasa National Steel Council, ta ware Naira miliyan 13; domin jin dadi da walwala. Haka nan, Ma’aikatar Ci Gaban Ma’adanai ta Kasa, ta ware Naira miliyan 126.37, a matsayin kudaden walwala da jin dadi, inda Shalkwatar Ma’aikatar ita ma; ta ware Naira miliyan 70, a matsayin kudaden walwala.
Har ila yau, hukumomin da ke karkashin wannan ma’aikata sun hada da; Hukumar Binciken Kasa ta Nijeriya, wadda ta yi hafzi da Naira miliyan 3.06, sai Ofishin Kula da Albarkatun Kasa da ya samu Naira miliyan 22.60, haka nan; Hukumar Asusun Habaka Ma’adanai (Solid Mineral Debelopment Fund), Naira miliyan 5.708, sai kuma Cibiyar Kula da Ma’adai ta Kasa, Naira miliyan 2.5.
Haka nan, Ma’aikatar Yawon Bude Ido ta tarayya; ita ma ba a bar ta a baya ba, wajen sanya wasu abubuwa da ake zargi na rashin gaskiya a cikin wannan kasafin kudi. Domin kuwa, Naira miliyan N491, 466, 376; aka ware a matsayin ‘yan kudaden kun ji-kun ji da kuma kudaden jin dadi da walwala a tashin farko. Wannan ma’aikata dai ta ware Naira biliyan 18, 867, 308, 651 a matsayin kasafinta na wannan shekara ta 2024.
Wannan sharholiya ta shafi har Ma’aikatar Fasaha, Al’adu da Tattalin Arziki da kuma hukumomin da ke karkashinta, domin kuwa hakan ya tabbata yayin da suka ware Naira miliyan 60,886,252, a matsayin kudaden walwala tare kuma da ayyana Naira miliyan 590,977,343, a matsayin kudaden ko-ta-kwana.
Haka zalika, gwamnatin tarayya ta sake ware Naira miliyan 251, 419, 160 a matsayin kudaden ko-ta-kwana da jin dadi da walwala na Ma’aikatar Harkokin Mata da kuma Cibiyar kula da matan ta kasa.
A cikin kundin kasafi na baya-bayan nan, gwamnatin tarayya ta ware Naira miliyan 355,065,055, domin tallafa wa hukumomin gwamnati da kuma fannin ilimi.
Cikakkun bayanai, sun hada da abin da ita kanta ma’aikatar da take a matsayin uwa za ta samu ita kadai, wato Naira miliyan 79,205,369, sai Cibiyar Tsare-tsare da Gudanar da Ilimi ta Kasa, Naira miliyan 40,451,885, inda Hukumar Kula da Dakunan Karatu ta Kasa (National Library of Nigeria), aka ware mata Naira miliyan 23,500,000, sai kuma Hukumar Ilimi ta Makiyaya Naira 500,000; ita kuma NERDC, Naira 36,514,584, sai kuma Hukumar Kula da Ilimin Kasuwanci da Kere-kere ta Kasa da ta samu Naira miliyan 3,665,435.
Duk da halin kuncin da ‘yan Nijeriya ke ciki a halin yanzu na matsin tattalin arziki, Ma’aikatar Raya Wasanni ta Tarayya, ta ware Naira biliyan 3,156 a cikin kasafin kudin wannan shekara, domin kula da walwala da abinci da jin dadi da shakatawa da kuma kula da sauran al’amuran da ka iya tasowa.
Baya ga Naira miliyan 9,387,143 da za a kashe a kan al’amuran jin dadi da walwala, kudaden da Minista zai kashe da Manyan Sakatarori sun dogara ne da abin da suke son kashewa.
Idan muka leka Ma’aikatar Kwadago da Aiki ta tarayya, ana bukatar Naira biliyan 2,638,634,610, don kyautata jin dadi da walwalar ma’aikatan da ke zaune a Shalkwatar Ma’aikatar da hukumominta, wanda duk da wadannan makudan biliyoyi da aka ware musu, bangaren ko-ta-kwana kadai suka fitar wa da kasafi.
A wani bangare kuma, Ma’aikatar Ruwa da Kula da Tsaftar Muhalli, ta samu Naira miliyan 37.14; don jin dadi da walwala a cikin wannan kasafi, yayin da kuma Ma’aikatar Neja Delta ta samu makudan kudade kimanin Naira miliyan 80,113,609, don jin dadi da walwalar ma’aikatanta, wanda aka kasa fayyace yadda za a yi a kashe wadannan kudade.
Takardar wannan kasafi da Jaridar LEADERSHIP ta samu, ya bayyana cewa; Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, ya ware Naira miliyan 398; don walwala da jin dadi a kasafin wannan kudi na shekarar 2024, yayin da Ministan Shari’a na tarayya da hukumomin da ke karkashinsa, aka ware musu zunzurutun kudade har Naira miliyan 180,151,316, domin jin dadi da walwala a cikin kasafin kudi na 2024.
Haka nan, Ma’aikatar Lafiya da Jin dadin Al’umma ita ma, an ware mata Naira miliyan 285, 582, 708, don jin dadi da walwala a cikin wannan kasafi, yayin da Ma’aikatar Muhalli kuma ta yi nata kasafin na Naira miliyan 301,068,141, domin walwala da jin dadi a kasafin shekarar 2024.
A bisa fama da matsananciyar yunwa da ‘yan Nijeriya da dama ke fuskanta, Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci ta Tarayya, an ware mata Naira miliyan 327,430,823, don inganta jin dadi da kuma walwala a cikin wannan kasafi na shekarar 2024 da aka amince da shi.