Idan aka yi nazari kan daukacin kasafin kudin Gwamnatin Tarayya da na jihohi na 2025, an lisaffa kasafin ne, kan dala 0.63, wanda kuma ya kai kasa da dala 2.15, da dan Nijeriya daya, zai iya kashe wa.
Wannan ya faru ne, kamar yadda Bankin Duniya ya ayyana cewa, talakan kasar, na cikin matsin talauci.
- Yadda Rasuwar Galadima Abbas Ta Haɗa Kawuna ‘Yan Siyasar Kano Masu Hamayya Da Juna
- Ofishin Siyasa Na Kwamitin Tsakiyar Jks Ya Kira Taron Nazarin Ayyukan Kiyaye Muhallin Halittu Da Sauransu
Hakazalika, wannan babban koma baya ne, musamman duba da yadda aka yi hasashen cewa, Nijeriya ce, kan gaba wajen fama da talauci.
An fitar da wannan bayanain ne, bisa wani sabon rahoto da wani Kamfanin yin bincike kan tattalin arziki na ADSR ya fitar a kan kasafin kudin na Gwamnatin Tarayya da kuma jihohi wanda duk dan Nijeriya daya, zai iya amfana wanda ya kai tsakanin daga dala 0.43 zuwa dala 0.21.
daukacin wannan adadin, ya kai kasa da daga kasa da dala 0.56 zuwa dala 0.36, sabainin na shekarar 2024.
“An tsara kasafin kudin na Gwamnatin Tarayya da na jihohin da dan Nijeriya daya zai amfana, musamman saboda talaucin da kasar ke ciki, bai wuce kasa da dala 2.15,”. Inji masu fashin bakin.
Kazalika, rahoton ya sanar da cewa, wannan ya nuna cewa, kasafin kudin na Gwamnatin Tarayya da na jihohin, ba za su iya biyan bukatun ‘yan kasar ba, musamman kan abinda ya shafi samun abinci, kula da kiwon lafiya da kuma samun ilimin zamani.
Kasafin kudin na Gwamnatin da dan Nijeriya day zai iya amfana, ya kai Naira 235,706, wanda hakan ke nuna cewa, kowanne dan Nijeriya daya, a kullum, zai iya kashe Naira 645.8, musamman idna har, kasafin kudin ya isa ga daukacin ‘yan kasar.
Hakazalika, a matakin jihohi kuwa, kasafin kudin, kowanne dan Nijeriya daya, a cikin shekara daya, zai iya kashe Naira 115,500, inda kuma a rana daya, kasafin ya kai Naira 317.
“Gaba dayan kasafin kudin na kasa, idan an rabawa ‘yan kasar, kowanne mutum daya, a cikin shekara daya, zai samu Naira 348,481 a cikin kasafin kudin na 2025, amma a nan, ana nufin idan kowanne dan kasar daya, zai iya samun Naira 955 a kullum daga cikin kasafin kudin,”. Acewar rahoton.
Kasafin kudin na 2025 a kan duk dan Nijeriya daya, ya nuna nawa ne, yawan jarin da Gwamantin Tarayya ta zuba kan dan kasar daya kuma nawa ne, ta shirya za ta kashe a kan kowanne dan Nijeriya daya.
karin fashin baki kan kasafin kudin na kasar na 2025 da ADSR ta yi, ya nuna cewa, jimlarsa da aka amince ya kai Naira tiriliyan 81.3.
Wannan ya hada da na Gwamnatin Tarayya da ya kai Naira tiriliyan 54.99 da kuma na jihohi da ya kai Naira tiriliyan 26.30, wanda hakan ya nuna cewa, an samu karin da ya kai na kaso 51.9, idan aka kwatanta da na shekarar 2024.
Kazalika, kasafin kudin na Gwamnatin Tarayya ya karu zuwa kaso The 56.9, inda kuma na gwamnatocin jihohin kasar, ya karu da kaso 42.4, musamman idan aka kwatanta da shekarar 2024.
Shugaban kasa Bola Tinubu, ta hanyar majalisar kasa ya kara yawan adadin kasafin kudin na bana daga Naira tiriliyan 49.7 zuwa Naira tiriliyan 54.2.
Bola ya yi hakan ne, domin ya kara bunkasa kashe kudade a kan manyan ayyuka, musamman duba da dakatar da tallafin jin kai, da da kasar Amurka, ke bai wa Nijeriya.
Sai dai, masu fashin bakin sun nuna damuwar su kan cewa, karain sama da Naira biliyan 700 a cikin kasafin kudin na shekarar 2025 da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta yi, ba zai samar da wasu sauye-sauyen azo a gani ba a kan tattalin arzikin kasar, musamman duba da ci gaba da biyan kudin ruwa na dimbin bashin da ake ci gaba da bin Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp