Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya bayyana a wajen taron manema labaru na ministan harkokin waje da aka shirya a harabar manyan tarukan kasar Sin guda biyu, lokacin da yake magana kan batun Taiwan cewa: suna daya tilo na Taiwan a Majalisar Dinkin Duniya shi ne “Lardin Taiwan na kasar Sin”. Kuma wasu sun yi amannar cewa, hakan ne ya sa manufar babban yankin kasar Sin a kan Taiwan ta zama mai tsaurin gaske.
Da take mayar da jawabi game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning, ta bayyana a wani taron manema labarai da aka saba gudanarwa da ya gudana yau 10 ga wata cewa, wannan shi ne daidaitaccen matsayin MDD a ko yaushe kuma haka abun yake a tarihi.
Mao Ning ta jaddada cewa, a ko da yaushe kasar Sin tana bin ka’idar kasancewar Sin daya tak, da kuma ra’ayi daya da aka samu na shekarar 1992, kana tana matukar son yin kokari don ganin an samu damar dinkuwar kasar Sin cikin lumana da gaskiya da sa himma. A sa’i daya kuma, kasar Sin za ta dauki dukkan matakan da suka dace don kare ikon mallakar kasarta da cikakken ‘yancin yankinta, da kuma fitowa da kakkausan harshe wajen nuna adawa da ayyukan ‘yan aware na neman ‘yancin kai na Taiwan da tsoma baki daga waje. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp