A yau, gwamnatin kasar Nauru ta sanar da katse huldarta ta “diplomasiyya” da yankin Taiwan. Bayan haka, ma’aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta ce, kasar Nauru ta sanar da amincewarta da manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, inda take neman maido da huldar diplomasiyya da kasar Sin. Dangane da batun, kasar Sin ta nuna yabo da maraba ga gwamnatin kasar Nauru.
Ma’aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta kara da cewa, kasar Sin guda daya ce tak a duniya, kana Taiwan wani yanki ne na kasar Sin da ba za a iya ballewa ba. Haka zalika, gwamnatin jamhuriyar jama’ar kasar Sin ita ce halastacciyar hukuma daya tak dake iya wakiltar daukacin kasar ta Sin. Wadannan bayanai, an riga an tabbatar da gaskiyarsu cikin kuduri mai lamba 2758 na babban taron MDD, wadanda suka kasance ra’ayi na bai daya na gamayyar kasa da kasa. A nata bangare, kasar Sin ta riga ta kulla huldar diplomasiyya da kasashe 182, bisa tushen yarda da manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya. Yadda gwamnatin kasar Nauru ke son maido da hulda da kasar Sin ya nuna cewa, manufar kasancewar kasar Sin daya tak tana samun cikakken goyon baya da amincewa a duniya.
Kasar Sin na son kaddamar da wani sabon babi na hulda da kasar Nauru, bisa tushen manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, in ji ma’aikatar harkokin waje ta kasar Sin. (Bello Wang)