Zamanin da muke ciki na samun ci gaba cikin hanzari ta fuskar kimiyya da fasaha yana ci gaba da shaida sabbin kere-kere da fasahohi na kara inganta gudanar da ayyuka a sassa daban-daban na rayuwar bil’adama. Daya daga cikin sassan da suke daukar hankali shi ne sashen sarrafa mutum-mutumi na kasar Sin.
Cibiyar Morgan Stanley da ke nazarin hidindimun kudi da sauran harkokin sarrafa dukiya mai hedkwata a birnin New York na Amurka, ta fitar da wani rahoto a watan Fabrairun da ya gabata game da masana’antun sarrafa mutum-mutumi a duniya, inda ya bayar da bayanai game da yanayin samar da mutum-mutumi a duniya. Rahoton ya nuna yadda kasar Sin ke taka rawar gani a fagen, saboda habakar da take samu wajen kere-keren mutum-mutumin musamman masu siffofin bil’adama.
- Xi Jinping Ya Halarci Bitar Tawagar Lardin Jiangsu
- An Koya Min Girmama Mata – Akpabio Ya Musanta Zargin Cin Zarafin Natasha
Rahoton na Morgan ya nuna cewa, kamfanonin kasar Sin ne suke da kashi 63 a cikin dari na dukkan mutum-mutumin da ake samarwa a duniya. Kana daga cikin adadin kamfanonin da ake da su a masana’antar, kashi 73 cikin dari a yankin Asiya suke, kuma kasar Sin ke da kashi 56 cikin dari a cikin adadin nasu.
Tun fiye da shekara 10 da suka gabata, kasar Sin ke kara samun habakar masana’antar kera mutum-mutumi. Rahoton da Kungiyar Samar da Mutum-mutumi ta Duniya (IFR) ta fitar game da harkokin kera mutum-mutumi na shekarar 2024, ya nuna cewa, kasar Sin ta yi wa kowa nisa a duniya wajen zama babbar katafariyar kasuwar mutum-mutumi ta duniya bisa yadda ta yi nasarar kakkafa masana’antun bangaren guda 276, 288 a shekarar 2023. Wannan ya sa kasar ta mallaki kashi 51 cikin dari na daukacin adadin masana’antun sashen da aka kafa a duniya.
Har ila yau, zuwa shekarar 2024, bayanan mahukuntan kasar Sin sun nuna a watan Yulin shekarar, kasar ta habaka fiye da sassa masu inganci da ke da alaka da mutum-mutumi 190,000, wanda hakan ke nuna kasar ce ke da kaso biyu bisa uku na daukacin wadanda ake da su a duniya.
Hakika, kasar Sin ta nuna bajinta a kan habakar da take samu a fagen kere-keren mutum-mutumi musamman ma a yayin bikin bazara na shekarar 2025 inda aka jero wasu mutum-mutumi 16 suka gudanar da raye-raye masu kayatarwa a wani bangare na shagulgulan jajibirin bikin. Yadda mutum-mutumin suka rika kwarkwasa da rawa da juyi ya yi matukar birge ’yan kallo na ciki da wajen kasar.
Bugu da kari, a karon farko, mutum-mutumi za su shiga a dama da su a wasan gudun fanfalakin da za a gudanar cikin watan Afrilu mai zuwa a Beijing, babban birnin kasar Sin, inda ake sa ran mutum-mutumin nan da aka saka masa fasahar kirkirarriyar basira ta AI, Tian Kung wanda cibiyar bunkasa kere-keren mutum-mutumi masu kirkirarriyar basira ta kasar Sin ta kera, na daga cikin wadanda za a fafata gudun da su. Duka dai, wannan yana kara fayyace ci gaban da kasar Sin take samu ne a fannin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp