Ma’aikatar al’adu da yawon bude ido ta kasar Sin ta bayyana cewa, a yayin lokacin hutun bikin Bazara na bana, an yi balaguro kusan miliyan 308 a cikin gida a kasar Sin, wanda ya karu da kashi 23.1 bisa dari kan na bara.
Alkaluman da ma’aikatar ta fitar sun nuna cewa, yawan kudaden shiga da aka samu a fannin yawon bude ido na cikin gida a lokacin hutun na tsawon mako guda, ya kai kudin Sin RMB Yuan biliyan 375.8, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 55.52, wanda ya karu da kashi 30 cikin dari kan na bara.
Jimillar wuraren shakatawa 10,739 dake mataki na A, dake zama kashi 73.5 cikin dari na jimillar wuraren bude ido na kasar, duk an bude su kamar yadda aka saba a lokacin hutun.
Alkaluman kudade na haraji sun nuna a jiya Juma’a cewa, yawan kudaden shiga da aka samu a bangaren sayarwa a sassan da ke da alaka a lokacin hutun bikin Bazara na tsawon mako guda, ya karu da kashi 12.2 bisa 100 idan aka kwatanta da na bara.
Haka kuma yawan kudaden shiga a fannin sayarwa, ya samu matsakaicin karuwar kashi 12.4 cikin 100 a cikin lokacin, idan aka kwatanta da lokacin hutun bikin Bazara na shekarar 2019, gabanin barkewar annobar cutar COVID-19, kamar yadda bayanan harajin da hukumar kula da harajin kasar ta fitar.(Ibrahim)