Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce ba abun mamaki ba ne, gano cewa Amurka na sa ido kan bayanan sirri a shafukan sada zumunta.
Kakakin ma’aikatar Wang Wenbin ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai na yau Talata, lokacin da yake tsokaci game da furucin shugaban shafin sada zumunta na Twitter, Elon Musk.
Rahotanni sun ruwaito cewa yayin wata zantawa da aka yi da shi, Elon Musk ya ce ya kadu, bayan ya gano cewa, gwamnatin Amurka na iya karanta sakonnin sirri na dukkanin masu amfani da shafin na Twitter.
A cewar Wang Wenbin, Amurka na zargin kamfanonin kasashen waje da sa ido da kuma satar bayanan Amurkawa ba tare da kwararan shaidu ba, inda ya ce yana kara bayyana ga duniya cewa, ikirarin Amurka na kare tsaron bayanai ba gaskiya ba ne, yayin da ta hakikance wajen tabbatar da babakere a kafar intanet. (Fa’iza)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp