A baya bayan nan, an jiyo wasu kusoshin gwamnatin Amurka na yawaita korafi, game da abun da suka kira “watsin da Sin ke yi da batun tattanawa da tsagin Amurka”. Cikin irin wadannan zarge-zarge, an jiyo wasu ’yan siyasar kasar na zargin cewa wai “Sin ta ki tsayar da sabon lokacin da ya dace sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya gudanar da ziyara a Sin”. Har ila yau, tsagin Amurka ya yi zargin cewa, ma’aikatar tsaron Sin ta ki ta amince da bukatar ma’aikatar tsaron Amurka na zantawa, yayin da kuma ministocin tsaron kasashen biyu suka shafe tsawon kusan watanni 5 ba su zanta da juna ba.
Bugu da kari, a yayin taron ministocin wajen kasashe mambobin kungiyar G7 da ya gudana a ’yan kwanakin baya a kasar Japan, an jiyo ministan harkokin wajen Amurka Antony Blinken na kira ga kasar Sin, da ta fayyace matsayarta game da alakarta da Amurka. Kana a cewarsa, sauran kasashen duniya na zuba ido don ganin sassan biyu sun daidaita alakarsu ta hanyar nuna sanin ya kamata.
To amma abun tambaya a nan shi ne, yayin da ake kokarin raya dangantakar kasashe daban daban, bangare daya ne ya dace ya nuna sanin ya kamata? Tabbas kowa ya san cewa “Ana iya kai Doki bakin ruwa, amma ba za a iya tilasa masa shan ruwa ba”. Ga misali, Amurka ce ta dage ziyarar da Mr. Blinken ya shirya kaiwa kasar Sin a watan Fabarairu, biyowa bayan surutai da suka rika bazuwa, game da harbo balan balan din nan ta kasar Sin da Amurka ta yi, kuma hakan ya auku ne daf da lokacin da Blinken din ke shirin tashi daga Amurka zuwa Sin.
Idan mun yi duba na tsanaki za mu ga cewa, Amurka ce ta dakatar da waccan ziyara bisa radin kanta, amma a yanzu take kokarin nunawa duniya tamkar Sin ce ke da alhakin dakatar da zuwan nasa. Wata tambayar ta daban ita ce, shin zai yiwu komai ya zama daidai da ra’ayin Amurka, kuma sai dai kowa ya bi ra’ayin ta yayin da ake hadin gwiwa?
Ko shakka babu kasar Sin babbar kasa ce dake da tarin hidimomin wanzar da ci gaban kanta, da ma kyautata hadin gwiwa da kasashen da suka rungumi tafiya irinta, don haka ba ta da lokacin batawa, ko shiga cacar baka, ko cece-kuce da wata kasa. Kaza lika salon diflomasiyyar kasar Sin na cike da muhimman ayyuka, wadanda ba zai yiwu a samu wata kafa ta biyewa bukatun Amurka ba, musamman ma batun da ya shafi shirya wata ziyara ga mutane masu kunbiya-kunbiya, ko wata boyayyar manufa.
Game da dalilin da ya sanya ministocin tsaron Sin da Amurka suka kwashe tsawon lokaci ba su zanta da juna ba kuwa, Amurka ta fi kowa sanin dalili, domin kuwa har yanzu ba ta janye takunkumai na rashin adalci da ta kakabawa sabon ministan tsaron kasar Sin janar Li Shangfu ba. Wanda hakan ya haifar da rashin kyakkyawan yanayi, da zai ba da damar tattaunawa tsakanin jami’an sojin kasashen biyu yadda ya kamata. Don haka idan har Amurka na son zantawa, ko tattaunawa da tsagin kasar Sin, to bai kamata ta dauki irin wannan mataki na raba gari ba.

Wani abun lura ma shi ne ita kanta Amurka, ta ganewa idanunta yadda a cikin watannin baya bayan nan, jagororin kasashe da dama, ciki har da na kawayenta, da shugabannin wasu hukumomin kasa da kasa suka rika ziyartar kasar Sin, tare da cimma kyakkyawan sakamako. Don haka abun tambayar a nan shi ne, me ya sa ake samun matsala da Amurka ita kadai a wannan fage?
Sinawa su kan ce “Saurari kalaman su ka kuma lura da ayyukan su”. To sai dai fa game da Amurka ta yau, kusan ma bata lokaci ne sauraren kalamanta, duba da yadda take furta maganganu tare da warware su ta hanyar aiwatar da matakai da suka saba da furucin nata. Don haka ana iya cewa, kalaman Amurka sun rasa kimarsu a idanun kasar Sin, da ma da yawa daga bangarorin kasa da kasa.

A baya bayan nan ma wasu rahotanni daga wasu kafofin watsa labaran Amurka, sun bayyana shirin gwamnatin kasar mai ci na aiwatar da wasu sababbin dokoki, wadanda a karkashinsu za ta tilastawa Amurkawa masu zuba jari, takaita yawan jarin da za su iya zubawa a kasar Sin. A hannu guda kuma, Amurka na kara tsoma baki cikin batun yankin Taiwan ba ji ba gani. Don haka ana iya cewa, matakan Amurka na kokarin dakile, ko mayar da kasar Sin baya na kara tsananta.
Duniya dai na ganin yadda kalaman jagororin Amurka ke sabawa ayyukan ta musamman game da batutuwan da suka shafi kasar Sin. Don haka zai yi wuya Sin ta amince da alkawuran dake fitowa daga bakin makusantan gwamnatin Amurka.
Ko shakka babu tattaunawa da cudanya suna iya bunkasa hadin gwiwa, kana suna yaukaka alakar sassa daban daban, kuma matakai ne na kandagarkin barkewar rikici ko takaita sabani. To sai dai kuma a bangaren ta, Washington tana boye manufarta karkashin wadannan kyawawan matakai, inda take son cimma moriyar siyasa ta hanyar abun da take kira “Tattaunawa da bangaren Sin”.

A nata bangaren kuwa, har kullum kasar Sin na daukar cudanyar ta da tsagin Amurka a matsayin wata babbar dama, ta kyautata dangantaka bisa hakuri da juriya, wanda hakan shi ne nauyin da Sin din ta runguma a matsayin ta na babbar kasa. Har ila yau, Sin na goyon bayan tattaunawa, da musaya bisa martaba juna, da rungumar matakan zaman lafiya, da hadin gwiwar cimma moriya tare, ta yadda za a kai ga yaukaka dangantakar Sin din da Amurka lami lafiya. Sai dai kuma akasari, shaidu na zahiri na nuna cewa, bukatar Amurka ta yin cudanya da Sin batu ne kawai na fatar baki, wanda take amfani da shi wajen jawo ra’ayi, da samun yardar kawayenta, da sauran kasashen da suke nuna matukar damuwa ga yanayin tabarbarewar alakar sassan biyu, yayin da a daya hannun Amurkan ke amfani da hakan wajen shafawa Sin kashin kaji.
Sanin kowa ne cewa, a shekarun baya bayan nan, ana ta fuskantar yanayi na rashin tabbas da kalubaloli daban daban a duniya, ta yadda hadin kai da cimma moriyar juna ya zama burin dukkanin kasashen duniya. Kaza lika sassan kasa da kasa sun fahimci cewa, kulla kawance da zai kare muradun kashin kai, ko katse hulda da wasu sassa, ko yakin cacar baka, ba za su haifarwa kowa da mai ido a yanayin da ake ciki ba. Shi yasa kasashen duniya daban daban ke kara rungumar tafiyar kasar Sin, duba da yadda take ta kara bude kofofin ta ga kasashen waje, da ci gaban da take samu tare da abokan huldar ta a bangarori daban-daban.
A baya bayan nan mun ga yadda shugabannin kasashe da dama ke ta kara amincewa da makomar hadin kansu da kasar Sin, matakin dake kara haifar musu da alherai masu tarin yawa.
Idan muka waiwayi tarihi, za mu ga tun bayan kafuwar janhuriyar jama’ar kasar Sin a shekarar 1949, Sin ba ta taba ruwa wutar yaki to haifar da hatsaniya ba, kana bata taba amfani da karfi domin mallakar wani yanki da ba nata ba. Kuma har zuwa yau, Sin ce kasa daya tilo a duniya, da ta sanya manufar samun ci gaba ta hanyar lumana cikin kundin tsarin mulkin ta.
Har kullum, burin kasar Sin shi ne martaba ikon mulkin kai, da ikon kasashe na kare cikakkun yankunan su. Kaza lika kasar Sin na matukar adawa da tsoma baki cikin harkokin gidan wasu kasashe na daban. Sabanin haka kuwa, wasu kasashen yammacin duniya na ganin duk wata kasa da ta samu ci gaba, akwai yiwuwar ta yi amfani da tasirin ta wajen yin babakere da nuna fin karfi.

Shaidu na zahiri sun nuna cewa, burin kasar Sin shi ne tabbatar da ci gaban duniya baki daya, a matsayin wani makami na warware dumbin matsaloli masu sarkakiya da bil adama ke fuskanta, kuma hakan ne ya sa Sin din ke sa kaimin yin hadin gwiwa da dukkanin kasashe, bisa shawarar nan ta “Ziri Daya Da Hanya Daya”, ta kuma gabatar da shawarar raya duniya baki daya.
Wani hasashe ma na bankin duniya ya nuna cewa, idan har aka yi nasarar aiwatar da dukkanin shirye-shirye na gina ababen more rayuwa ta fannin sufuri, karkashin shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”, ya zuwa shekarar 2030, hakan zai rika samar da kudaden shiga har dalar Amurka tiriliyan 1.6 a kowace shekara, yayin da kuma kasashen da suka rungumi shawarar za su ci gajiyar kimanin kaso 90 bisa dari na kudaden. Don haka dai muna iya cewa, bunkasuwar kasar Sin, dama ce ga kowa ba wai kalubale ba!
Alal hakika, kyautata hulda tsakanin Sin da Amurka, mataki ne da zai inganta moriyar kasashen biyu, zai kuma haifar da kwanciyar hankali da bunkasar tattalin arzikin duniya baki daya. Kuma ko kadan, Sin ba abokiyar gabar Amurka ba ce. Don haka kamata ya yi a yi watsi da ra’ayin yakin cacar baka, ko burin cin nasara daga hasarar wani bangare, maimakon hakan, ya dace sassan biyu su kyautata huldar su bisa turbar zaman lafiya da lumana. Kuma ko shakka ba bu wannan ita ce matsayar kasar Sin.
Ana iya ganin hakan a zahiri, idan aka dubi yadda kasar Sin ta karbi bakuncin shugabannin duniya da dama a ‘yan makwannin baya bayan nan, ciki har da shugaban kasar Gabon Ali Bango Ondimba, wanda a yayin ziyarar sa a Sin, shi da shugaba Xi Jinping suka amince da kudurin daga matsayin cikakkiyar dangantakar hadin gwiwa tsakanin kasashen su, zuwa cikakkiyar dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare.
Kafin ziyarar shugaban na Gabon, Sin ta karbi bakuncin shugabannin kasashen Faransa, da na Brazil, da shugabar tarayyar Turai, baya ga firaministocin kasashen Sifaniya, da Malaysia, da Singapore. Kaza lika a baya bayan nan shugaba Xi Jinping ya zanta ta watar tarho da shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy, inda suka yi musayar ra’ayi game da halin da ake ciki don gane da rikicin kasar ta Ukraine, da ma yadda ya dace a shawo kan rikicin bisa turbar diflomasiyya.
Daga karshe, wasu masharhanta na ganin jan kafar da Amurka ke yi game da batun hawa teburin shawara ba wani abun damuwa ba ne, domin kuwa, har kullum kofofin kasar Sin a bude suke, kuma duk lokacin da Amurka ta nuna hali na dattaku, ta aiwatar da matakai na zahiri, abu ne mai sauki a koma kan teburin shawara, da musayar ra’ayoyi a fannoni daban daban tsakanin ta da Sin, wanda hakan ne hakikanin burin kasashen duniya game da alakar sassan biyu.