Yau Asabar 1 ga watan Yuni, sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin, ya yi amfani da tattaunawar Shangri-La a matsayin wata dama ta baje kolin Amurka, inda ya yi tsokaci kan “Tsarin Indo-Pacific”, da batutuwan da suka shafi yankin Taiwan.
Game da haka, bangaren Sin ya bayyana cewa,“Tsarin Indo-Pacific” na Amurka, yana karkashin dalilin wai inganta hadin gwiwar yanki, amma a zahiri yana bin tunanin yakin cacar-baka, da ra’ayin samun riba kan asarar wani bangare ne, da aiwatar da matakan kullewa, da kebance kai.
- Tsarin Kiwon Lafiyar Yaran Kasar Sin Na Kara Kyautata, In Ji Jami’ar Hukumar Lafiyar Kasar
- Hanya Mafi Sauki Da Za A Magance Matsalar Tsaro A Katsina – Gamayyar Kungiyoyin Arewa
Ainihin manufar ita ce hada kananan rukunoni cikin babbar kungiyar NATO, sashen Asiya-Pacific, don wanzar da matsayin danniya ko yin babakere wanda Amurka ke jagoranta.
Batun Taiwan, batu ne mafi muhimmanci a jigon dangantakar Sin da Amurka. A cikin ‘yan shekarun nan, Amurka ta yi watsi da alkawuran da ta dauka, da yin fatali da manufar Sin daya tilo a duniya, kana ta taimakawa yankin Taiwan neman ‘yanci, da ba shi makamai, da hargitsa yanayin da mashigin tekun Taiwan ke ciki.
Rundunar sojojin kasar Sin ta PLA, ba za ta amince da ballewar Taiwan daga kasar Sin ba, kuma yunkurin neman ‘yancin Taiwan daidai yake da tayar da yaki. Kaza lika rundunar soja ta PLA, ba za ta daina horar da sojoji don share fagen yaki ba, kana ba za a dakatar da yaki da yunkurin neman ‘yancin Taiwan, da inganta dinkewar kasar daya ba, har ila yau ba za ta sassauta wajen murkushe tsoma baki cikin harkokin gida, da wasu kasashen waje suke yi ba. Ko shakka babu kasar Sin za ta tsaya haikan, wajen sauke nauyin dake wuyanta, na kiyaye mulkin kai da cikakken yankin kasa. (Bilkisu Xin)