Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau Alhamis cewa, kasarsa ba za ta canza niyyartar ba, ta ci gaba da fadada bude kofa ga kasashen waje, da kirkiro wani yanayi na gudanar da kasuwanci mai bin doka da oda, wanda zai amfani kasuwanni da sassan kasa da kasa.
Wang ya ce, a shekaru 10 da suka gabata, duk da cewa ra’ayin bangaranci, da na bada kariya ga kasuwanni na ci gaba da yaduwa a duniya, kasar Sin ba ta taba dakatar da kokarinta na raya sabon tsarin tattalin arziki dake kara bude kofa ga kasashen waje ba, wanda hakan ya sa sassan kasa da kasa suke more damammakin ci gaban kasar Sin, kuma kasuwar Sin ta zama tamkar ta kowa da kowa.
Kwanan nan saboda rikicin makamashi, kasashen Turai da dama sun dakatar da yunkurin daina amfani da kwal, da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli.
Game da tambayar da aka yi masa, dangane da ko kasar Sin za ta ci gaba da nuna kwazo wajen rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli, Wang ya ce, kasar ba za ta canza niyyarta ba, ta samar da ci gaba mai dorewa ba tare da gurbata muhalli ba. (Murtala Zhang)