Jami’i a ma’aikatar sufuri ta kasar Sin Gao Haiyun, ya ce Sin ta zamo ta daya a duniya, a fannin yawan manyan jiragen ruwa, idan aka yi la’akari da jimillar dakon da jiragen ruwan kasar ke gudanarwa.
Gao ya ce a yanzu haka, jiragen ruwa mallakin ’yan kasuwar kasar na dakon hajojin da suka kai tan miliyan 249.2. Kaza lika a shekarar 2022 da ta gabata kadai, kayayyakin da jiragen ruwa na dakon kaya da tashoshin jiragen ruwan kasar suka karba, sun kusa kaiwa nauyin tan biliyan 15.7, kana sundukan dakon kaya masu tsayin kafa 24, da tashoshin suka karba sun kai kwatankwacin miliyan 296. Kuma wadannan alkaluma duk sun kai matsayin koli a duniya cikin shekaru masu yawa.
Har ila yau, jami’in ya ce kusan kaso 95 bisa dari na jimillar hada-hadar cinikayyar waje ta Sin, suna gudana ne ta ruwa. Yayin da kasar ke gudanar da hada hadar sufuri ta hanyoyin ruwa tsakaninta da sama da kasashe da yankunan duniya 100, wadanda suka hade daukacin gabobin kasashen da yankunan na ruwa, bisa tsarin “ziri daya da hanya daya”. (Saminu Alhassan)