Ma’aikatar kula da cinikayya ta kasar Sin, ta ce kasar na adawa da yadda Amurka ke danne kamfanoninta bisa fakewa da batun tsaron kasa.
Kakakin ma’aikatar madam He Yongqian ce ta bayyana haka yayin wani taron manema labarai game da binciken da Amurka ke yi kan kamfanin TP-Link mai kera na’urar samar da sadarwar intanet ta Router, bisa fakewa da batun tsaron kasa.
A cewar madam He, ya kamata Amurka ta kasance mai tsare gaskiya yayin aiwatar da irin wannan bincike, maimakon yin zarge-zarge mara tushe saboda irin abubuwan da take aikatawa. (Fa’iza Mustapha)