Game da sabuwar shawarar inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma, wadda kasashen G7 suka gabatar, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yau Litinin cewa, kasarsa har kullum tana maraba da duk wata shawarar dake inganta muhimman ababen more rayuwar al’ummar duniya, kana shawarwari daban-daban ba za su iya maye gurbin juna ba.
Ya ce kasar Sin na nuna adawa ga duk wani yunkuri na bata sunan shawarar “ziri daya da hanya daya”, bisa hujjar inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma, don cimma muradun siyasa.
Rahotanni sun ce, kwanan nan, a wajen taron kolin kasashen G7, shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya sanar da kaddamar da “dangantakar abokantaka ta inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma da zuba jari a duniya”, kana wasu manyan jami’an gwamnatin Amurka da ba’a san ko su waye ba, sun rika furta kalamai na shafawa shawarar “ziri daya da hanya daya” ta kasar Sin bakin fenti.
Rahotannin sun kuma ce, a ranar 25 ga wata, wani jami’in kwamitin tsaron kasa na fadar White House ta Amurka mai suna John Kirby, ya yi magana kan taron kolin kasashen G7, inda ya sake jaddada batun da ya shafi wai “yin aikin tilas” a kasar Sin.
Game da wannan batu, Zhao Lijian ya ce, yin aikin tilas, ba a kasar Sin yake faruwa ba, a Amurka yake wakana. Sai dai domin neman cimma muradunta na amfani da batun jihar Xinjiang, don kawo cikas ga ci gaban kasar Sin, Amurka ta sha kitsa karairayi dake cewa wai, ana tilastawa al’umma aiki a Xinjiang. Amma hakikanin gaskiya ita ce, irin zargin da Amurka ta yiwa kasar Sin, ya shaida laifin da ita kanta take aikatawa. (Murtala Zhang)