Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya mayar da martani game da al’amari, wato an kashe shugaban kungiyar Hamas Ismail Haniya a wani hari a Tehran, fadar mulkin kasar Iran. Lin Jian ya bayyana cewa, kasar Sin na adawa, da kuma yin Allah wadai da kisan gilla. Tana kuma matukar damuwa kan tsanantar rashin zaman lafiya a yankin Gabas na Tsakiya sakamakon faruwar lamarin. (Bilkisu Xin)