Ministan kula da harkokin cinikayya na kasar Sin Wang Wentao, ya kasarsa ba ta gamsu da matakin Amurka na kakaba karin harajin kaso 10 kan kayayyakinta bisa kafa hujja da batun maganin Fentanyl ba.
Wang Wentao ya bayyana haka ne cikin wata wasikar taya murna da ya aikewa Howard Lutnick, sabon sakataren Amurka kan harkokin cinikayya.
- Wang Yi Ya Bayyana Ra’ayin Sin Kan Yadda Za A Karfafa Huldar Cude-Ni-In-Cude-Ka A Duniya
- Dangote Ya Koma Matsayi Na 86 A Jadawalin Masu Arziƙin Duniya
A cewar ministan, kasashen Sin da Amurka sun yi tattaunawa mai zurfi tare da hada hannu kan batun dakile tu’ammali da Fentanyl, kuma an samu kyawawan sakamako. Yana mai cewa, harajin da Amurka ta kakaba ya kawo tsaiko ga dangantakar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin kasashen biyu.
Ya kara da cewa, kasar Sin na fatan za a shawo kan batutuwan dake ciwa kowannensu tuwo a kwarya ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna bisa adalci. (Mai Fassara: Fa’iza Mustapha)