Kasar Sin ta bayyana adawa tare da sukar matakin Amurka, na sanya wasu kamfanonin kasar cikin jerin wadanda ba za a fitar musu da kyayyaki daga Amurka ba.
A jiya Alhamis ne Amurka ta sanar da kara wasu kamfanonin Sin 37 cikin jerin, tana mai zarginsu da shiga cikin wasu harkokin Soja da na Rasha.
- Mukalar Shugaba Xi: Hakika Kasar Sin Ba Ta Yi Wa Duniya Rowar Kaifin Basirarta Ba
- Peng Liyuan Da Mai Dakin Firaministan Kasar Hungary Sun Ziyarci Makarantar Koyar Da Harsunan Sinanci Da Hungary
Cikin wata sanarwa a yau, kakakin ma’aikatar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin, ya ce Amurka ta dade tana fakewa da batun tsaron kasa wajen takaita fitar da kayayyaki domin dannewa ko dakile ci gaban kamfanonin kasashen waje.
A cewarsa, matakin ya keta halaltattun hakkoki da muradun kamfanonin, da yin tsaiko ga tsaro da karkon tsarin samar da kayayyaki da masana’atu na duniya, da kuma yin cikas ga farfadowa da bunkasar tattalin arzikin duniya.
Har ila yau, yayin taron manema labarai na yau Juma’a, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya shaidawa manema labarai cewa, Amurka tana gazawa wajen gabatar da shaida a duk lokacin da ta yi amfani da batun “tsaron kasa” wajen danne kamfanonin kasar Sin.
Ya kara da cewa, Sin da Rasha na da ‘yancin gudanar da hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya, wanda bai kamata a dakile ko a haifar masa da cikas ba. (Fa’iza Mustapha)