• English
  • Business News
Tuesday, August 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasar Sin Na Allah Wadai Da Harin Da Aka Kai Wa Ma’aikatan Agaji Na Kasa Da Kasa A Gaza

by CGTN Hausa
1 year ago
in Daga Birnin Sin
0
Kasar Sin Na Allah Wadai Da Harin Da Aka Kai Wa Ma’aikatan Agaji Na Kasa Da Kasa A Gaza
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Labarai Masu Nasaba

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Majalisar Dokokin Rasha

Sin Ta Bukaci Japan Ta Waiwayi Tarihin Kutsen Da Ta Yi

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wang Wenbin ya bayyana a jiya Talata cewa, kasarsa na adawa da duk wani danyen aiki na illata fararen-hula da kayyayakin more rayuwarsu, wanda kuma ya sabawa dokokin kasa da kasa. Haka kuma, tana tir da harin da aka kai wa ma’aikatan agaji na kasa da kasa a zirin Gaza, tare da jajen rayukan da aka rasa.

Jami’in ya ce, Sin ta bukaci bangarori masu ruwa da tsaki, musamman Isra’ila, da su aiwatar da kuduri mai lamba 2728 na kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya a zahirance, da sauke nauyin da kundin tsarin mulkin MDD ya danka musu, da tsagaita bude wuta ba tare da bata lokaci ba, a wani kokari na kiyaye fararen-hula da ba su ji ba su gani ba, da tabbatar da tsaron al’umma gami da kayyayakin amfaninsu bisa Yarjejeniyar Geneva, ciki har da asibiti, don kaucewa ta’azzarar bala’in jin-kai a zirin na Gaza.

  • Xi Jinping Da Joe Biden Sun Tattauna Ta Wayar Tarho
  • Ba Shakka Kamfanonin Ketare Za Su Ci Riba In Suka Zuba Jari Da Aiwatar Da Ayyukansu A Sin

Game da harin ta’addancin da aka kai kan tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa na Dasu da kamfanin kasar Sin ke gniawa a kasar Pakistan a ranar 26 ga watan Maris, Wang ya ce, kasar Sin na tuntubar Pakistan sosai game da wannan batu, don ganin an hukunta ‘yan ta’addan da suka kai harin.

A kwanan nan ne wato ranar 1 ga watan Afrilu, firaministan kasar Pakistan, Muhammad Shahbaz Sharif ya yi tattaki zuwa tashar Dasu don mika gaisuwa da fatan alheri ga ma’aikatan kasar Sin dake wurin, inda ya yi alkawarin cewa, kasarsa za ta yi iya bakin kokarinta wajen kare tsaron Sinawa gami da ayyukan da suke yi, da yanke hukunci mai tsanani kan wadanda suka kai harin. (Murtala Zhang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Fintiri Ya Nada Farfesa Gidado Da Wasu 4 Hukumar Gudanarwar Jami’ar Adamawa

Next Post

Sojoji Na Zargin Sarakuna Da Hannu A Kisan Dakaru 17 A Delta

Related

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Majalisar Dokokin Rasha
Daga Birnin Sin

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Majalisar Dokokin Rasha

1 hour ago
Sin Ta Bukaci Japan Ta Waiwayi Tarihin Kutsen Da Ta Yi
Daga Birnin Sin

Sin Ta Bukaci Japan Ta Waiwayi Tarihin Kutsen Da Ta Yi

1 hour ago
Xi Da Uwargidansa ​​Sun Gana Da Sarkin Cambodia Da Mahaifiyarsa Sarauniya
Daga Birnin Sin

Xi Da Uwargidansa ​​Sun Gana Da Sarkin Cambodia Da Mahaifiyarsa Sarauniya

3 hours ago
Sassou Nguesso: Muna Fatan Gaggauta Tabbatar Da Sakamakon Taron Beijing Na FOCAC
Daga Birnin Sin

Sassou Nguesso: Muna Fatan Gaggauta Tabbatar Da Sakamakon Taron Beijing Na FOCAC

5 hours ago
Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harbar Rukunonin Taurarin Dan Adam 10 
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harbar Rukunonin Taurarin Dan Adam 10 

5 hours ago
An Yi Bikin Mu’ammalar Al’Adu Na SCO Na 2025 A Beijing
Daga Birnin Sin

An Yi Bikin Mu’ammalar Al’Adu Na SCO Na 2025 A Beijing

22 hours ago
Next Post
Sojoji Na Zargin Sarakuna Da Hannu A Kisan Dakaru 17 A Delta

Sojoji Na Zargin Sarakuna Da Hannu A Kisan Dakaru 17 A Delta

LABARAI MASU NASABA

Hatsarin Jirgin Kasa: Gwamna Uba Sani Ya Ba Da Umarnin Talllafawa Fasinjojin Da Ke Cikin Jirgin

Hukumar NRC Ta Dakatar Da Zirga-zirgar Jiragen Kasa Na Abuja zuwa Kaduna

August 26, 2025
Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Majalisar Dokokin Rasha

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Majalisar Dokokin Rasha

August 26, 2025
Sin Ta Bukaci Japan Ta Waiwayi Tarihin Kutsen Da Ta Yi

Sin Ta Bukaci Japan Ta Waiwayi Tarihin Kutsen Da Ta Yi

August 26, 2025
Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 128 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Zamfara

Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 128 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Zamfara

August 26, 2025
Xi Da Uwargidansa ​​Sun Gana Da Sarkin Cambodia Da Mahaifiyarsa Sarauniya

Xi Da Uwargidansa ​​Sun Gana Da Sarkin Cambodia Da Mahaifiyarsa Sarauniya

August 26, 2025
Hatsarin Jirgin Kasa: Gwamna Uba Sani Ya Ba Da Umarnin Talllafawa Fasinjojin Da Ke Cikin Jirgin

Hatsarin Jirgin Kasa: Gwamna Uba Sani Ya Ba Da Umarnin Talllafawa Fasinjojin Da Ke Cikin Jirgin

August 26, 2025
Sassou Nguesso: Muna Fatan Gaggauta Tabbatar Da Sakamakon Taron Beijing Na FOCAC

Sassou Nguesso: Muna Fatan Gaggauta Tabbatar Da Sakamakon Taron Beijing Na FOCAC

August 26, 2025
Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harbar Rukunonin Taurarin Dan Adam 10 

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harbar Rukunonin Taurarin Dan Adam 10 

August 26, 2025
Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna Ya Yi Hatsari, Ba A San Halin Da Fasinjoji Ke Ciki Ba

Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna Ya Yi Hatsari, Ba A San Halin Da Fasinjoji Ke Ciki Ba

August 26, 2025
Saka Zai Yi Jinyar Makonni 4 Sakamakon Rauni Da Ya Samu A Wasan Leeds

Saka Zai Yi Jinyar Makonni 4 Sakamakon Rauni Da Ya Samu A Wasan Leeds

August 26, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.