Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Lin Jian, ya bayyana a yau Alhamis cewa, kasarsa ta yaba da jawabin shugaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya yi tir da harin ta’addancin da aka kai wa Pakistan, jawabin da ya shaida babbar aniyar kasa da kasa wajen yakar ta’addanci. Kaza lika, kasar Sin tana adawa da duk wani yunkuri na aikata ta’addanci, da mara wa Pakistan baya wajen daukar matakan murkushe ayyukan ta’addanci.
Rahotanni sun ruwaito cewa, kwamitin sulhu na MDD ya fitar da jawabin shugabansa a jiya Laraba, inda ya yi Allah wadai da harin ta’addancin da aka kai yankin Besham dake lardin Khyber Pakhtunkhwa na kasar Pakistan.
Bugu da kari, a yayin da yake amsa tambayar da ta shafi martaninsa kan furucin ministan harkokin wajen New Zealand, Lin Jian ya ce, kamar sauran kasashe masu rungumar zaman lafiya, kasar Sin ita ma tana damuwa matuka kan dangantakar AUKUS dake tsakanin kasashen Amurka da Birtaniya da kuma Australiya, wato “dangantakar abota ta fuskar tsaro tsakanin bangarorin uku”. Ya ce Sin na fatan ganin bangarori masu ruwa da tsaki sun kara aikata abubuwan alheri don taimakawa samun fahimtar juna da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. (Murtala Zhang)