Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya bayyana yau Laraba a gun taron manema labaru da aka saba yi cewa, kasarsa na farin cikin ganin yadda aka gudanar da babban zaben kasar Senegal cikin lumana da kwanciyar hankali, tare da taya Bassirou Diomaye Faye, murnar nasarar da ya samu.
Rahotanni sun bayyana cewa, dan takarar jam’iyyar BBY ta Senegal Amadou Ba, ya fitar da sanarwa a ranar 25 ga wata, inda ya amince da shan kaye da ya yi, tare da taya dan takarar jam’iyyar adawa Bassirou Diomaye Faye murna.
- Wang Yi Ya Gana Da Baki Amurkawa Bi Da Bi
- Kasar Sin Ta Kasance Ja Gaba Wajen Lalubowa Duniya Sabbin Damarmakin Ci Gaba
Game da wannan batu, Lin Jian ya bayyana cewa, Sin da Senegal abokai ne, kuma ‘yan uwan juna. Ya ce kasar Sin tana mai da hankali sosai kan raya dangantakar dake tsakaninta da Senegal, kuma tana son yin aiki tare da sabuwar gwamnatin kasar, wajen zurfafa amincewa da juna a fannin siyasa, da fadada hadin gwiwa a zahirance, da kuma kara ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba.
Har ila yau, Lin Jian ya sanar da cewa, bisa gayyatar Wang Yi, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kuma ministan harkokin wajen kasar, ministan harkokin wajen kasar Benin Shegun Adjadi Bakari, zai kawo ziyarar aiki kasar Sin tun daga ranar 28 ga watan Maris zuwa 1 ga watan Afrilu. (Mai fassara: Bilkisu Xin)