Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, da takwaransa na kasar Masar Sameh Shoukry, sun zanta ta wayar tarho a jiya Litinin, game a rikicin Falasdinu da Isra’ila, da kuma batun hadin gwiwar raya ziri daya da hanya daya.
Yayin tattaunawar da suka yi, mista Shoukry ya nuna damuwa game da yanayin da ake ciki game da rikicin Falasdinu da Isra’ila, ya kuma jinjinawa kasar Sin bisa nacewa ka’idojin ta, da goyon bayan adalci, da marawa Falasdinawa baya game da burin su na karbo halastaccen hakkin mulkin kai, da kafuwar kasa mai cin gashin kai.
A nasa bangare kuwa, Wang cewa ya yi a matsayin Masar na muhimmiyar abokiyar tafiya, a hadin gwiwar raya shawarar ziri daya da hanya daya, Sin na da karfin gwiwa cewa, Masar din za ta taka rawar gani wajen cimma nasarar taron hadin gwiwar raya shawarar, da ma cimma burin samar da hadin gwiwa mai nagarta, a fannin raya manufar ziri daya da hanya daya.
Sannan wakilin dindindin na kasar Sin a MDD, Zhang Jun, ya yi kira da a tsagaita bude wuta tsakanin kasar Isra’ila da bangaren Falasdinawa, don kare fararen hula. Zhang ya yi kiran ne yayin taron kwamitin sulhun MDD da ya gudana a jiya Litinin.
Ya ce fada ya barke tun a kwanan baya tsakanin sassan biyu, wanda kuma ya yi sanadin rasa rayukan dimbin fararen hula, da haifar da matsala a fannin ayyukan jin kai, tare da haifar da mummunan tasiri ga yanayin tsaron daukacin yankin baki daya, lamarin da ya sa kasar Sin nuna damuwa sosai.
Jami’in ya kara da cewa, kasar Sin ta yi Allah wadai da duk wani mataki na lahanta fararen hula, da adawa da duk wani aiki na sabawa dokokin kasa da kasa. (Masu Fassara: Saminu Alhassan, Bello Wang)