Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana a yau Jumma’a cewa, kasarsa tana goyon bayan Siriya wajen tabbatar da zaman lafiya tun da wuri, kuma tana goyon bayan kasar wajen samar da shirin sake gina kasar, da zai dace da muradun al’ummar kasar ta hanyar tattaunawa da bangarorin da abin ya shafa.
Wang ya bayyana hakan ne a lokacin da aka yi masa tambaya game da ra’ayin kasar Sin kan halin da ake ciki a kasar Siriya, yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da ministan harkokin wajen Masar Badr Abdelatty, bayan tattaunawarsu kan manyan tsare-tsare na Sin da Masar a Beijing.
- Xi Ya Gabatar Da Muhimmin Jawabi A Babban Taron Ayyukan Tattalin Arziki Na Tsakiya
- Tinubu Zai Gabatar Da Kasafin Kuɗin 2025 Da Ya Kai ₦47.9trn
Wang ya kara da cewa, kamata ya yi a nan gaba kasar Siriya ta yi tsayin daka wajen nuna adawa da duk wani nau’in ta’addanci da masu tsattsauran ra’ayi. Kuma a halin da ake ciki, ya kamata kasashen duniya su kiyaye ’yancin kan Siriya da cikakken yankinta, da mutunta al’adunta na gargajiya da addini, tare da baiwa al’ummar kasar damar yanke shawarwari bisa kashin kansu.
Wang ya kuma yi karin haske kan matsayin kasar Sin game da tashe-tashen hankula a yankin gabas ta tsakiya. Yana mai cewa babban aikin da aka sanya gaba shi ne tsagaita bude wuta nan da nan, da dakatar da tashin hankali, da sassauta matsalar jin kai. Kana babbar hanyar samar da mafita ita ce sasantawa ta hanyar siyasa da sake dawo da shawarwari da tattaunawa, kuma muhimmiyar ka’idar ita ce goyon bayan ’yancin kai da kauce wa tsoma baki daga waje.
A ranar 13 ga wata ne Wang Yi, ya jagoranci taron tattaunawa kan manyan tsare-tsare na ministocin harkokin wajen Sin da Masar tare da Badr Abdelatty a birnin Beijing, inda ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta karfafa tuntubar juna da hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare da kasar Masar, don ba da gudummawa tare wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, da sa kaimi ga ci gaban duniya baki daya. (Mohammed Yahaya)