Jiya Asabar 2 ga wata ne, aka bude taron baje kolin kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2023, game da hada hadar cinikayyar ba da hidima ko CIFTIS a birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, inda ya nuna cewa, tattalin arzikin duniya yana bunkasa idan an bude, kuma yana raguwa idan an rufe shi.
Shekarar da muke ciki shekara ce ta cika shekaru 45 da aka soma yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje. A cikin shekaru kusan 50 da suka wuce, irin matakin da Sin ta dauka ba wai kawai ya sauya kasar sosai ba, har ma ya yi babban tasiri ga duniya baki daya. Bari mu dauki cinikayyar hidima a matsayin misali, kasar Sin ta kara fadada kayayyakin da take shigo da su daga kasashen waje, tare da samar da babbar kasuwa mai yawan jama’a biliyan 1.4 don cinikin hidima a duniya. Bayanai sun nuna cewa, a cikin shekaru 15 da suka gabata, kayayyakin hidima da kasar Sin ta shigo da su daga kasashen waje sun kai dalar Amurka tiriliyan 4.5, wanda ya haifar da karuwar kashi 10.4 cikin 100 na kayayyakin hidima da ake shigo da su a duniya.
A sa’i daya kuma, kasar Sin ta yi nazari kan sabbin fasahohin da aka samu na cinikayyar hidima a duniya ta hanyar bude kofa a fannin tsare-tsare, kuma CIFTIS na daya daga cikinsu. Tun lokacin da aka fara shi a shekarar 2012, CIFTIS ya jawo hankalin masu baje kolin fiye da 600,000 daga kasashe da yankuna 196, da kuma kungiyoyin kasuwanci da hukumomi na kasashen waje fiye da 600. A baje-kolin na bana, kasashe 51 da kungiyoyin kasa da kasa 24 sun gudanar da nune-nunen, kamfanoni sama da 2200 ne suka halarci taron, kuma manyan kamfanoi 500 da suka fi fice a duniya da ma manyan kamfanonin dake kan gaba sun halarci taron.
A yayin da yake jawabi a taron baje kolin din, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da cewa, kasarsa za ta karfafa da fadada bude kofa ga kasashen waje, da kuma samar da sabbin dammamaki ga kasa da kasa wajen bude kofa ga juna da kuma gudanar da hadin gwiwa. Baya ga haka, ya yi kira ga kasashe daban daban da su more damammakin ci gaban cinikayyar hidimar duniya, da kuma tura tattalin arzikin duniya kan hanyar farfadowa mai dorewa. (Mai fassara: Bilkisu Xin)