Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce kasar na maraba da kwararru daga dukkan fadin duniya, kuma ta na fatan za su ci gaba da shiga ana damawa da su sosai, a ayyukan raya kasar Sin.
Li Qiang ya bayyana haka ne a babban dakin taron jama’a dake Beijing, yayin da yake ganwa da baki kwararru wadanda suka samu lambar yabo ta abota ta gwamnatin kasar Sin da ake bayarwa ga baki kwararrun da suka yi fice a kasar Sin.
- CMG Ta Kaddamar Da Bikin Fara Nuna Shirin “Journey Through Civilizations” A Hong Kong Da Macau
- Kaunar Da Xi Jinping Yake Nuna Wa Gari, Dangi Da Kuma Al’ummar Kasa
Firaministan ya kuma yabawa kyakkyawar gudunmuwar da suke bayar wajen inganta ci gaban kimiyya da fasaha da horar da jami’ai da zamantar da kasar Sin
A nasu bangare, kwararrun ‘yan kasashen waje sun bayyana godiyarsu da samun lambar yabon da kuma kudurinsu na ci gaba da bayar da gudunmuwa ga aikin zamanatar da kasar Sin da ma inganta musaya da hadin gwiwa tsakanin Sin da sauran kasashe. (Fa’iza Mustapha)