Idan wani abokinka yana zuwa gidanka don gaishe ka, da nuna fatan alheri a farkon duk wata sabuwar shekara, cikin shekaru 33 a jere. Shin kauna da sahihanci da ya nuna maka za su burge ka?
A kwanan baya, ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ya yi ziyara a kasashen Habasha, da Gabon, da Angola, da Benin, gami da Masar, wadda ta kasance ziyara ta farko da jami’in ya yi, bayan da ya hau mukamin ministan wajen kasar Sin. Kana ya zama shekaru 33 a jere, da ministan waje na kasar Sin ya kai ziyara a nahiyar Afirka a farkon duk shekara. Hakan ya shaida dadadden zumuncin da ake da shi tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, da sahihancin da kasar Sin ta nuna ma abokanta dake nahiyar Afirka.
Wannan sahihanci, shi ne tushen hadin gwiwar Sin da Afirka, wanda ya tabbatar da yanayin hadin gwiwa na amfanar da juna, da haifar da ci gaba ga dukkan bangarorin kasashen Afirka da kasar Sin:
Tun daga shekarar 2000, kasar Sin ta gina layin dogo fiye da kilomita 6000, da hanyoyin mota na kilomita 6000, da tashoshin jiragen ruwa kimanin 20, da manyan tashoshin samar da wutar lantarki fiye da 80, a kasashen Afirka. Gami da ba da tallafin asibitoci fiye da 130, da makarantu fiye da 170, da dakunan wasannin motsa jiki 45, da ayyukan aikin gona fiye da 500 a nahiyar Afirka.
Kaza lika a kasuwannin kasar Sin, yanzu ana iya ganin gahawa, da kayayyakin hannu, da dai sauransu, wadanda aka samar da su a kasashen Afirka, wadanda suka taimakawa inganta zaman rayuwar Sinawa.
Yayin da minista Qin Gang ke ziyara a kasar Habasha a wannan karo, ya halarci bikin kammala ginin babbar cibiyar hana yaduwar cututtuka ta nahiyar Afirka. Wannan aiki shi ma ya shaida sahihancin da kasar Sin ta nuna ma kasashen Afirka.
Yayin barkewar annobar cutar Ebola a yammacin Afirka a shekarar 2014 ma, kasar Sin ta samar da tallafi ga kasashen da annobar ta shafa, da kungiyar kasashen Afirka ta AU, ba tare da jinkiri ba. Daga baya kuma, Sin ta sanar da samar da gudummawar gina ginin babbar hedkwatar cibiyar hana yaduwar cututtuka ta nahiyar Afirka kyauta, don tallafawa kokarin kasashen nahiyar na kare lafiyar jama’arsu.
Yanzu hakan dai an mika wa kungiyar AU, manyan bangarori na wannan babban gini wanda fadinsa ya kai muraba’in mita dubu 90, wanda aka kashe dalar Amurka miliyan 80 wajen gina shi. Wannan babbar kyauta ta nuna yadda kasar Sin take samar wa kasashen Afirka da hakikanin taimakon da ake bukata, ba tare da gindaya wani sharadi ba. Kana duk wani alkawarin da kasar Sin ta yi, to, za ta cika shi.
Ban da wannan kuma, ana iya ganin sahihancin da kasar Sin ta nuna, bisa yadda ta ki yarda da yunkurin siyasantar da batun hadin gwiwa da kasashen Afirka. A lokacin da yake hira da manema labaru, tare da shugaban kwamitin kungiyar AU Moussa Faki Mahamat, Mista Qin Gang ya ce, “Afirka dandali ne na hadin gwiwar kasa da kasa, maimakon fagen takarar manyan kasashe. Idan dole ne a yi takara, to, ya dace a duba wace kasa ta fi samar da gudunmowa ga kokarin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a nahiyar Afirka, gami da taimakawa kasashen Afirka, samun karin wakilci da ikon fada a ji a fannin kula da al’amuran kasa da kasa. ” A cewarsa, duk wata kasa, idan ta nuna sahihanci, na tabbatar da samun zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki a nahiyar Afirka, to, kasar Sin za ta mara mata baya.
Hakika kokarin hadin gwiwa da kasashen Afirka da kasar Sin take yi, ya riga ya janyo karin jari zuwa nahiyar Afirka, daga kasashen yamma. Yayin da wani masani dan Najeriya mai suna Ovigwe Eguegu ke hira da manema labaru a kwanan baya, ya ce, manyan shirye-shiryen zuba jari na “Huldar abokai ta gina kayayyakin more rayuwa da zuba jari ko (PGII)” na kungiyar G7, da shirin “Kofofin duniya” (Global Gateway) na kungiyar tarayyar Turai na EU, an gabatar da su ne, bayan da aka ga yadda shirin “Ziri daya da hanya daya ko (B&R)” na kasar Sin ke yin muhimmin tasiri a duniya.
Sai dai kasashen yamma sun ki yarda da sahihancin kasar Sin, har ma kafofin watsa labarun su na cewa wai kasar Sin, ta jefa kasashen Afirka cikin “tarkon bashi”. Dangane da wannan zargi, Mista Qin Gang ya mayar da martani ta hakikanan bayanai.
A cewarsa, kasar Sin ta yi kokarin halartar shirin dakatar da biyan bashi karkashin laimar kungiyar G20, inda ta kulla yarjejeniya, ko kuma cimma ra’ayi tare da kasashe 19 dake nahiyar Afirka, a fannin dakatar da biyan bashi, lamarin da ya sanya kasar zama mafi samar da sakamako a wannan fanni, cikin mambobin kungiyar G20.
A sa’i daya kuma, wani rahoto daga bankin duniya ya nuna cewa, hukumomin hada-hadar kudi na kasa da kasa, da ‘yan kasuwa masu ba da bashi, suna rike da kashi 3 cikin kashi 4 na dukkan bashin da ake bin kasashen Afirka. Saboda haka Mista Qin ya bukaci wadannan hukumomi, da mutane da su kara taka rawa a fannin sassauta matsalar bashi a kasashen Afirka.
Hakika dalilin da ya sa kasashen yamma ba za su yarda da sahihanci na kasar Sin ba, shi ne domin akwai bambancin ra’ayi tsakaninsu. A ganin mutanen kasashen yamma, moriyar kai ta fi muhimmanci, amma tunanin da kasar Sin ta daukaka shi ne, kafa al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya. A ganin Sinawa, wasu manyan matsaloli sun shafi duniya baki daya, kana babu wata kasa da za ta iya kare kai, ba tare da hadin gwiwa da sauran kasashe ba. Saboda haka, ya kamata a lura da damuwar sauran kasashe, yayin da ake neman tabbatar da moriyar wata kasa, gami da ciyar da tattalin arzikin kasashe daban daban gaba, yayin da ake neman raya kai.
Wannan tunani shi ne ainihin dalilin da ya sa kasar Sin ke ta nuna cikakken sahihanci ga abokanta dake nahiyar Afirka. (Bello Wang)