Bikin baje kolin hada-hadar ba da hidima na kasa da kasa wato CIFTIS a takaice na shekarar 2025 da aka rufe a yau Lahadi, ya ja hankalin masu saka jari daga tarin kasashen waje. Manyan jami’an kamfanoni na kasashen waje sun bayyana cewa, suna daukar bikin a matsayin wata babban dandamali na more damammaki tare da kasar ta Sin.
Game da dalilan da suka sa ake zabar kasar Sin don gudanar da hada-hadar kasuwanci, mataimakin babban darekta mai kula da harkokin gwamnati da manufofi na kasar Sin na kamfanin Johnson & Johnson Mr. Zhao Jun ya ce, “Da farko shi ne, don biyan bukatun gaggawa na Sinawa kimanin miliyan 1400 a fannin kiwon lafiya. Na biyu a Sin akwai wani muhallin kasuwanci dake inganta ci gaban kamfanonin kasashen waje, wanda kuma ke kara samun kyautatuwa. Na uku, mun gano cewa, kirkire-kirkiren da kasar Sin ke yi na kara wa kamfanonin aikin jinya kwarin gwiwar samun bunkasa. Bisa wadannan dalilan uku ne kamfanin Johnson & Johnson zai dada gudanar da kasuwancinta a kasar Sin.”
A matsayinta na babbar bakuwa a gun bikin baje kolin, kasar Australia ta kafa rukunin nune-nune mafi girma a tarihinta tun bayan ta fara halartar bikin. Game da haka, mataimakin babban jami’in zartarwa na kwamitin cinikayya da zuba jari na kasar Daniel Boyer, ya bayyana cewa, sana’o’in ba da hidima na da matukar muhimmanci, wadanda suka kasance karfin da ba za a iya rabuwa da shi ba a ci gaban dangantakar dake tsakanin Australia da Sin. (Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp